Kasafin kudin Buhari: Za a sayi janareta na N104bn, aikin wutar Mambila kuma N650m

Kasafin kudin Buhari: Za a sayi janareta na N104bn, aikin wutar Mambila kuma N650m

  • Yayin da 'yan Najeriya ke tunanin wutar lantarki za ta daidaita a 2022, gwamnati ta karya gwiwar 'yan kasa
  • Rahoto ya bayyana irin makudan biliyoyin da gwamnati ta ware domin sayen janareta da hidimarsa
  • A baya gwamnati ta bayyana a kasafin kudin cewa, ta ware wasu miliyoyi domin aikin wutar Mambila

Abuja - Mafarkin samun wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya na kokarin gushewa kafin zuwan shekarar 2022 duba da yadda gwamnatin Buhari ta ware makudan kudi saboda saye da tattala janareta.

Wannan ya biyo bayan matakin da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya suka shigar na kashe kimanin Naira biliyan 104 wajen sayen janareto, man fetur da yi musu hidima a shekarar 2022.

Cikakkun bayanai na kunshe ne a cikin kudirin kasafin kudin shekarar 2022 wanda har yanzu majalisar dokokin kasar ba ta gama amince da shi ba.

Kara karanta wannan

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

Kasafin kudin Buhari: Za a sayi janareta na N104bn, aikin wutar Mambila kuma N650m
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin gabatar da kasafin kudi | Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

A zahiri, jaridar Punch ta ba da rahoton cewa adadin na iya karuwa kamar hukumomi kusan 15 basu ambaci bukatarsu ta janaretan ba.

Daga cikin hukumomin akwai hukumar jarrabawa ta JAMB, Bankin Muhalli na Najeriya, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa da Hukumar Fasaha ta kasa.

Hakazalika ciki har da Hukumar Fansho ta kasa, Hukumar Kwastam ta Najeriya, Babban Bankin Najeriya, Majalisar Jarabawa ta Kasa, Babban Bankin Najeriya da dai sauransu.

Gwamnatin Buhari ta ware miliyoyin kudi domin aikin wutan Mambilla a shekarar 2022

Gwamnatin tarayya ta yi kasafin Naira miliyan 650 a matsayin kasonta na kwangilar wutar lantarkin Mambilla a shekarar 2022 mai zuwa.

A tsarin yarjejeniyar aikin wutan Mambilla, gwamnatin tarayya da kasar Sin za su yi karo-karo domin ayi wannan aiki da ake lissafi zai ci Dala biliyan 5.

Kara karanta wannan

Amurka ta gano sirri: 'Yan bindiga na hada kai da Boko Haram don bata gwamnatin Buhari

Jaridar Daily Trust tace kasa da Naira biliyan daya gwamnatin tarayya ta ware wa wannan aikin.

Aikin na Mambilla yana cikin muhimman ayyukan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ci burin yi, ganin ta yi alkawarin inganta harkar wuta a Najeriya.

Kasafin kudin 2022 ya wuce karatu na biyu a majalisar wakilai

A wani labarin, Daily Trust ta rahoto cewa, majalisar wakilai a ranar Alhamis 14 ga watan Oktoba ta zartar da kasafin kudin 2022 na naira tiriliyan 16.39 don wuce karatu na biyu na majalisa.

Wannan ya biyo bayan kammala muhawara kan manyan ka'idojin kasafin na shekarar 2022.

Majalisar dattijai, a ranar Laraba, ta zartar da Dokar Kasafin Kudi ta 2022 a karatu na biyu bayan sama da awa daya ana muhawara kan manyan ka'idojin ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.