Bidiyon otal a kasan ruwa wanda ake biyan N28m na kwana 1 ya janyo cece-kuce
- 'Yan Najeriya suna ta maganganu kan wani bidiyon dakin hotal da ake biyan $50,000 daidai da N28 miliyan a kwana daya
- Dakin hotal din shi ne na farko da aka taba yi a kasan ruwa kuma ya na nan a tsibirin Rangali da ke Maldives
- Yayin da wasu ke kallon wurin a matsayin aljannar duniya, wasu suna cewa akwai tsada kuma akwai matukar hatsari
Bidiyon wani hotal da ke kasan ruwa ya janyo maganganu daban-daban a shafukan sada zumunta.
An tattaro yadda hukumar hotal din ke karbar zunzurutun kudi har $50,000 wanda yayi daidai da N28 kowacce rana.
Hotal din Muraka na kasan ruwa shi ne na farko irin shi da aka taba yi a duniya kuma ya na wani bangaren na wurin shakatawa da ke tsibirin Rangali da ke Maldives.
Wani bidiyon da aka bayyana cikin dakunan otal din, tsarin kawar da ke cikin dakunan baccin abun kallo ne kuma ya kai nisan kafa 16 cikin tekun Indiya.
Tsarin ginin abun kallo ne inda aka bayyana bandaki, falo kuma ya na bai wa wadanda ke cikin otal din damar kallon dukkan cikin tekun Indiya.
'Yan Najeriya sun yi martani
@lovewoluofficial ta ce: "Tirkashi! wannan abu ya yi kyau. Idan na shiga wurin nan tare da masoyi na, me zai sa mu bata? Tuna irin rayuwar dadin da muka yi a wurin nan kadai ya isa ya share min hawaye."
@iamsexysteel ta rubuta: "28 miliyan... kawai saboda in kwanta in tashi? Ko dai mutum zai gan shi a aljanna ne? Sannan kuma irin wannan otal din lokaci a guje ya ke tafiya kamar sun shirya komai"
Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen
@mama_xino tsokaci ta yi da: "Wannan ba irin nawa ba ne. Ba zan iya rufe ido ba a cikinsa. Babu lallashin da za a yi min da zai sa in iya bacci."
Direba ya mayar wa 'yan kasuwa N500,000 da suka manta da ita a Kekensa
A wani labari na daban, wani matukin Keke ta haya mai suna Mallam Tulu, ya mayar da kudi har N500,000 zuwa ga wasu 'yan kasuwa bayan sun manta da shi a abun hawansa a Jos, jihar Filato.
Kamar yadda wani Bello Lukman na Unity FM Jos ya wallafa a shafinsa na Facebook, 'yan kasuwan su na kan hanyarsu ta zuwa siyan shanu a yankin Yanshanu da ke Jos a ranar Asabar, 16 Oktoba yayin da suka manta da kudin.
"Allah ya albarkaci Mallam Tulu, matukin Keke wanda ya dawo wa da fasinjojin 'yan kasuwa kudi har dubu dari biyar da suka manta da su a Kekensa a Jos," ya ce.
Asali: Legit.ng