Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

  • Shugaba Buhari ya bayyana cewa, karshen 'yan bindiga ya zo, kuma za a ragargaje su nan kusa
  • Ya bayyana haka ne yayin da ya yi Allah wadai da harin 'yan bindiga a wani yankin jihar Sokoto
  • Ya kuma bayyana cewa, sojoji na sake shirin don ci gaba da ganowa da kuma hallaka 'yan bindigan

Abuja - Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindiga cewa su kasance a shirye don murkushe su ya zo kusa.

Shugaban ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin 18 ga watan Oktoba yayin da yake mayar da martani kan kisan sama da mutane 30 a Goronyo, Jihar Sakkwato ranar Lahadi.

Buhari ya fusta da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwananakinku sun kusa karewa
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Buhari, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, ya ce kwanakin 'yan bindiga a kirge suke saboda karfin da sojojin Najeriya ke samu ta hanyar samun kayan aiki da sauran bukatu.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Yadda 'yan bindiga suka yi wa jama'a kisan kiyashi a kasuwar Sokoto

Ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya:

"Kada su yanke kauna saboda wannan gwamnatin ta himmatu fiye da kowane lokaci wajen kare 'yan Najeriya daga kungiyoyin masu aikata kisan gilla wadanda ba sa girmama kimar rayuwar dan adam."

Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda harin Goronyo ya rutsa da su sannan ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hakuri yayin da sojoji ke nemo yadda za su kai wa wadannan ‘yan bindiga hari.

Ya ce:

“Lokacin halakar ku yana tafe saboda ba za ku sake samun wurin buya ba.

Amurka ta gano sirri: 'Yan bindiga na hada kai da Boko Haram don bata gwamnatin Buhari

Wani kwamitin kasar Amurka ya bankado yadda 'yan ta'addar Boko Haram da ke aiki a Arewa maso Gabas ke hada kai da 'yan bindiga da ke addabar al'ummomin Arewa maso Yamma don karbar kudin fansa daga gwamnatin Buhari da fararen hula.

Kara karanta wannan

Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen

Wannan na zuwa ne daga cikin rahoton wata jaridar Amurka mai suna The Wall Street Journal a ranar Asabar 16 ga watan Oktoba.

Jaridar ta Amurka ta ba da rahoton cewa Amurka ba ta mai da hankali kan 'yan bindiga a matsayin barazana kai tsaye ga muradun ta ba, sai dai, jami'ai na sa ido kan kwamandojin 'yan ta'addan da ke hada kai da mayakan Boko Haram.

Sojoji na gina rugar Fulani a kudu: Rundunar soji ta yi martani kan jita-jita

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar da ke yawo mai cewa, a halin yanzu wata runduna na gina matsugunar Fulani a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Jita-jitar da ake yadawa ta ce, runduna ta 82 ta sojin Najeriya tana aikin gina rugar Fulani a tsakanin Ochima da Affa a cikin Igbo-Etiti da Udi na jihar Enugu.

A cikin wata sanarwar da Legit.ng Hausa ta samu a ranar Laraba 13 ga watan Oktoba dauke da sa hannun Manjo Abubakar Abdullahi, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar, rundunar sojin Najeriya ta watsi da batun.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen jihohin Najeriya 12 da UK ta shawarci 'yan kasar ta da su kiyaya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.