Miyagun yan bindiga sun kutsa dakin kwana sun yi awon gaba da wani hamshaƙin dan kasuwa a Arewa

Miyagun yan bindiga sun kutsa dakin kwana sun yi awon gaba da wani hamshaƙin dan kasuwa a Arewa

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun shiga har ɗakin kwanan wani ɗan kasuwa, Abdu Yarima, sun yi garkuwa da shi a Jalingo
  • Majiya ta tabbatar da cewa maharan ba su tada hankalin kowa ba, suna zuwa kai tsaye suka nufi gidan abin harinsu dake yankin Kasuwan Yelwa
  • Wasu maharan kuma sun yi garkuwa da wata matar aure a cikin gidan mijinta, duk a cikin kwaryar birnin Jalingo

Taraba - Yan bindiga sun sace wani ɗan kasuwa, Abdu Yarima, har cikin ɗakin da yake kwana a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Dailytrust ta rahoto cewa maharan sun mamaye gidan ɗan kasuwan ne dake yankin Kasuwan Yelwa, a cikin kwaryar birnin Jalingo, ranar Lahadi da daddare.

Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan na isowa yankin, kai tsaye suka dumfari gidan ɗan kasuwan inda abun harinsu yake.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Yan bindiga
Miyagun yan bindiga sun kutsa dakin kwana sun yi awon gaba da wani hamshaƙin dan kasuwa a Arewa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta gano cewa sai bayan da yan ta'addan suka kammala abinda suka zo yi gidan, sannan iyalan ɗan kasuwan suka samu damar neman taimako.

Mahara sun sace wata matar Aure

Hakazalika, yan bindiga sun yi awon gaba da wata mata a gidan mijinta dake kusa da Kogin Mallam Garba, duk a cikin birnin Jalingo.

Rahoto ya bayyana cewa mijinta, Sadanu Sani, ya taba shiga hannun masu garkuwa a nan gidan a farkon wannan shekarar, amma ya kuɓuta bayan an biya su kuɗin fansa.

Yan ta'addan da suka addabi mutane a yankin suna amfani ne da Kogin Malam Garba a matsayin hanyar zuwa maɓoyarsu dake cikin duwatsu a Kundo, ƙaramar hukumar Ardo Kola.

Me hukumar yan sanda tace game da lamarin?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, bai ɗaga kiran waya da aka jera masa ba, hakanan kuma bai turo amsar sakonnin SMS da aka tura masa.

Kara karanta wannan

An kuma, Miyagun yan bindiga sun kutsa fadar Basarake, sun yi awon gaba da shi a jihar Katsina

A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun sake bude wa mutane wuta a kasuwar jihar Sokoto

Wata majiya daga garin ta bayyana cewa yan ta'addan sun kai hari da adadi mai yawa na mutane ranar Lahadi da daddare, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Rahoto ya nuna cewa har zuwa yanzun ba'a san adadin yawan mutanen da harin ya shafa ba, amma mutane da dama sun mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262