Wani matashi ya hallaka ɗan shekara 50 da ya kama a dakin budurwarsa suna biɗala

Wani matashi ya hallaka ɗan shekara 50 da ya kama a dakin budurwarsa suna biɗala

  • Kishi yasa wani matashi kashe ɗan shekara 50 da ya kama tare da budurwarsa a ɗakinta
  • Rahoto ya nuna cewa mutanen biyu suna neman mace ɗaya, inda shi matashin ya kama ɗayan a ɗaki , yasa wuka ya sare shi
  • Kakakin yan sanda, Abimbola Oyeyemi, yace matar da ake rigima a kanta ta tsere ba'a san inda take ba

Ogun - Jami'an yan sandan jihar Ogun sun damƙe wani matashi ɗan shekara 25, Bisi Omoniyi, bisa zargin kashe abokin takararsa a ɗakin matar da suke nema.

Dailytrust ta ruwaito cewa jami'an sun samu damar kama wanda ake zargin ne bayan kiran gagawa da aka musu ta caji ofis ɗin dake Owode Egbado.

A rahoton da yan sandan suka samu, an bayyana musu cewa wani matashi ya sheƙe wani mutumi da adda a garin Ajilete dake karamar hukumar Yewa ta arewa, jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Kara Kaɗa Hanjin PDP Kan Wanda Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

Jihar Ogun
Wani matashi ya hallaka ɗan shekara 50 da ya kama a dakin budurwarsa suna biɗala Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa manema labarai cewa bayan samun wannan rahoto ne, nan take DPO Owode Egbado da CSP Olabisi Elebute, suka tura jami'an sintiri yankin, suka cafke matashin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace da farko an yi gaggawar kai mutumin da aka sara da adda zuwa Asibiti, amma daga baya likiti ya tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Oyeyemi ya ƙara da cewa a binciken da yan sanda suka gudanar sun gano cewa wanda aka kashe Akinyemi Wahab, ya ziyarci ɗaƙin abokiyar baɗalarsa, Kafayat Sakariyau, domin kwana a ɗakinta.

Yace wanda ake zargin, shima yana neman wannan matar, ya kawo mata ziyara kamar yadda ya saba domin rage dare amma sai aka hana shi shiga, kamar yadda Punch ta rahoto.

Yadda lamarin kisan ya faru?

Kara karanta wannan

Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi

Kakakin yan sandan yace:

"Ganin an hana shi shiga ya ɓata masa rai, ya ɓalle kofar da karfin tsiya ya shiga, amma yanayin da ya tsinci budurwar tasa da mutumin ba zai iya jurewa ba, kamar yadda ya faɗa."
"Daga nan sai suka fara kokawa tsakaninsu, matashin ya ɗauki adda a ɗakin ya kafta masa sara, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa."
"A halin yanzun an kai gawar ɗakin aje gawarwaki, yayin da matar da aka aikata kisan a kanta ta tsere, ba'a san inda ta yi ba."

A wani labarin kuma Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa

Wani magidanci a ƙasar Indiya ya nemi a raba aurensa da matarsa shekaru biyu da aure, saboda bata yin wanka kullum.

Sai dai labarin baiwa matar ɗaɗi ba, inda ta garzaya wurin wata ƙungiyar kare mata, tana neman a ceto mata aurenta.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Tsohon Ɗan Majalisar Dokoki a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262