Jerin sunaye: Manyan 'yan ta'adda da shugabannin 'yan bindiga 12 da aka sheke a 2021
Duk da yadda ta'addanci ke kamari a kasar Najeriya, wasu daga cikin manyan cigaban da aka samu a shekarar nan su ne sheke shugabannin 'yan ta'adda.
A cikin wannan shekarar, a kalla 'yan ta'adda 12 da suka hada da na Boko Haram da 'yan bindiga suka rasa rayukansu yayin da dakarun sojin Najeriya suka tsananta yakarsu.
Ga jerin sunayen shugabannin 'yan ta'adda da aka kashe a shekarar 2021. Wannan rubutun ya yi dogaro ne da takardun da rundunar sojin Najeriya da kafofin yada labarai suka ruwaito.
1. Abubakar Shekau
Bayan shekaru da aka dauka ana cewa ya mutu kuma daga baya ya na bayyana, an ruwaito cewa Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram ya mutu a watan Mayu.
Kamar yadda TheCable ta wallafa, an gano cewa Shekau ya rasa ran sa ne bayan ya tada bam da ke jikinsa ganin cewa 'yan ta'addan ISWAP suna son ya yi musu mubaya'a.
2. Abu Mus’ab Albarnawi
A ranar Alhamis da ta gabata, shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, ya tabbatar da kisan shugaban ISWAP, Abu Musab Al-Barnawi.
Al-Barnawi dan Mohammed Yusuf ne, asalin shugaban Boko Haram wanda aka kashe a shekarar 2009.
3. Yaya Ebraheem
PR Nigeria ta ruwaito cewa Yaya Ebraheem ya na daga cikin manyan kwamandojin ISWAP da suka yi yunkurin kai wa tawagar sojoji farmaki a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba a Ngamdu da ke Borno.
A wurin kuwa dubunsa ta cika inda rundunar ta sheke shi har lahira.
4. Baba Chattimari
Baba Chattimari, wani gagarumin kwamandan kungiyar ta'addanci ta ISWAP ne kuma an sheke shi tare da Yaya Ebraheem.
5. Abu Adam Oubaida
Abu Adam Oubaida shi ne kwamandan ISWAP na uku da aka sheke yayin da suka kai wa sojoji farmaki a Ngamdu.
6. Auwalun Daudawa
Auwalun Daudawa gawurtaccen shugaban 'yan bindiga ne da ya jagoranci satar yara 300 na GSS Kankara a jihar Katsina a Disamban shekarar da ta gabata.
Daudawa ya yada makamansa a watan Fabrairun da ta gabata kuma ya rungumi zaman lafiyan da Gwamna Matawalle ya bukata.
Bayan kwanaki kadan, Daudawa ya koma daji inda ya cigaba da barna. Hakan ce ta sa rikici ya barke tsakaninsa da makiyaya har suka sheke shi, Channels TV ta ruwaito.
7. Jauro Daji
Jauro Daji wani fitaccen dan bindiga wanda ya addabi jama'a jihar Neja. Jami'an tsaro tare da taimakon 'yan banga ne suka kashe shi tare da wasu 'yan bindiga mabiyansa da ke Kontagora a ranar 30 ga watan Augusta.
8. Habu Nabayye
9. Isuhu Sadi
10. Murtala Danmaje
Nabayye, Sadi da Danmaje gagaruman shugabannin 'yan bindiga ne a jihar Zamfara.
Kamar yadda PR Nigeria ta ruwaito, an kashe su ne sakamakon luguden wuta da sojin saman Najeriya suka yi a dajin Kuyanbana.
11. Alhaji Karki Buzu
12. Yalo Nagoshi
PR Nigeria ta ruwaito cewa an kashe Buzu da Nagoshi ne a watan Oktoba a jihar Neja. Suna daga cikin 'yan bindiga 32 da suka tsero daga jihar Zamfara sakamakon luguden dakarun sojin Najeriya.
Asali: Legit.ng