Jarumin Gwamna El-Rufai ya bayyana abinda ke matukar tsorata shi
- Jajirtaccen gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce rashin tsaron da arewa maso yamma ke ciki ya na firgita shi
- El-Rufai ya ce idan ya tuna cewa 'yan Boko Haram su na tattarowa tare da komowa arewa maso yamma, ba ya jin dadi
- Ya yi kira da a hada kai a magance matsalar, saboda daga arewa maso yamma, zai yuwu su koma wani yankin
Ekiti - Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce yankin arewa maso yamma an shiga rudani ganin cewa akwai yuwuwar 'yan ta'addan Boko Haram su tattaro komatsansu daga arewa maso gabas, su dawo nan.
Ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron da gwamnatin jihar Ekiti ta shirya mai suna ‘Fountain Summit’.
A watan Mayun da ta gabata, 'yan ta'addan ISWAP sun halaka Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, TheCable ta ruwaito.
Duk da tuni ake ta yada rade-radin mutuwar Shekau, tun daga watan Mayu, ba a sake samun bidiyon shugaban Boko Haram ba.
TheCable ta wallafa cewa, a yayin jawabi, gwamnan jihar Kaduna ya ce ya dace dukkan 'yan Najeriya su damu da lamarin tsaro ba tare da duban yankin da matsalar ta shafa ba.
El-Rufai ya kara da cewa, duk da Kaduna ta na fuskantar kalubalen tsaro, masu zuba hannayen jari sun san cewa kadarorin su na tsare.
"Muna da kalubalen tsaro, amma masu zuba hannayen jari sun san cewa kadarorinsu na tsare. Ba mu taba ganin kanun labaran tsaro sun dakile mana hannayen jari ba," yace.
"Amma dole ne mu yi aiki tare wurin inganta tsaro. Dole ne mu daina 'mu da su' kuma mu hada kai.
El-Rufai ya kara da cewa:
“Idan za ku tuna, lokacin Boko Haram ta shafi arewa maso gabas kadai ne. Yanzu babban abun tsoronmu shi ne yadda Boko Haram ke tattarawa suna dawowa yankin arewa maso yamma saboda yadda ake fatattako su daga arewa maso gabas.
“Idan aka fatattake su a yankin arewa maso yamma, ina ku ke tsammanin za su tafi? Can wani wuri. Abu ne da ya dace duk mu damu da shi, ba gwamnatin tarayya da na jihar ba, dukkan fadin kasar nan ya dace mu damu.
“Ka da ku ga abinda ke faruwa a jihar Kaduna ku ce ba matsalar ku ba ce. Wata rana zai zama matsalar ku idan ba a shawo kan shi ba."
Kaduna: 'Yan bindiga sun sako 3 daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da suka sata
A wani labari na daban, uku daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da aka sace na Christ the King Major Seminary a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna sun samu 'yancinsu.
Kamar yadda Daily Trust ta ruiwaito, shugaban makarantar, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da sakin su da aka yi a daren Laraba.
Ya ce cocin za ta cigaba da addu'a tare da fatan a sako sauran daliban da ke hannun masu garkuwa da mutanen.
Asali: Legit.ng