Wani Uba Ya ga Ta Kansa a Kano, Yaran da Ya Haifa Sun Kai Shi Kotu kan Dukiyarsa

Wani Uba Ya ga Ta Kansa a Kano, Yaran da Ya Haifa Sun Kai Shi Kotu kan Dukiyarsa

  • Wani fitaccen attajiri a jihar Kano, Alhaji Isma’ila Mai Biskit, ya bayyana rikici ya ɓarke tsakaninsa da wasu daga cikin ’ya’yansa kan batun dukiyarsa
  • Dattijon ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan ya yanke shawarar sayar da wasu daga cikin kadarorinsa domin neman lafiya a ƙasashen waje
  • A cewarsa, yana cikin cikakken hayyacinsa, bai taɓa hauka ba, kuma babu wanda ya tilasta masa sayar da kadarorinsa, yana mai gargaɗin zai ita tsinewa yaran

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Fitaccen attajiri kuma dattijo a jihar Kano, Alhaji Isma’ila Mai Biskit, ya shiga wani hali na damuwa da ƙunci, bayan dambarwa a cikin iyalinsa har ta kai gaban kotu.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin ’ya’yansa sun kai shi kotu bisa zargin cewa bai da cikakken ikon yanke shawara kan dukiyarsa.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari ta fallasa yadda aka so korar ta, ’ya’yanta daga fadar shugaban kasa

Wasu yara sun kai mahaifinsu kotu
Taswirar Kano, jihar da aka samu wasu yara sun kai mahaifinsu kotu Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dattijon ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Freedom Radio, wadda daga bisani aka wallafa a shafin Facebook na gidan rediyon.

Dattijo a Kano ya koka da 'ya 'yansa

Alhaji Isma’ila ya ce Allah SWT ya jarrabe shi da rashin lafiya mai tsanani, har ta kai ga ya yanke shawarar zuwa Dubai domin neman magani.

A sakamakon haka, ya ce ya sanya ɗaya daga cikin kadarorinsa a kasuwa, ciki har da sayar da kamfaninsa da ya assasa tun yana saurayi, wato Bagauda Biskit.

Sai dai a cewarsa, wannan mataki bai yi wa wasu daga cikin ’ya’yansa daɗi ba, lamarin da ya sa suka ɗauki zafi suka kai ƙara ofishin ’yan sanda a Abuja.

Yaran da suka kai kara suna zargin cewa an tilasta masa sayar da dukiyar ba da son ransa ba, har su ke neman kotu ta taka masa burki daga amfani da kadararsa.

Kara karanta wannan

Abba Fiya: 'Dan daban da ya kashe mutum sama da 100 ya shiga komar yan sandan Kano

Martanin dattijon kan zargin ’ya ’yansa

Da yake mayar da martani, Alhaji Isma’ila Mai Biskit ya karyata dukkannin zarge-zargen da ake yi. Ya ce a da hankalinsa, kuma babu wanda ya yi masa tilas sayar da dukiyarsa domin neman lafiya ba.

Yan sandan Abuja sun kama yaran wani dattijo a Kano
Sufeton yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto; Nigeria Police Force
Source: Facebook

Ya bayyana cewa:

“Ban taɓa yin hauka ba, kuma tsufa na bai kai matakin da zan rasa hankalina ba. Ina cikin cikakken hayyacina, kuma da kaina na yanke shawarar sayar da dukiyar domin neman lafiya.”

Dattijon ya kuma musanta zargin cewa wasu daga cikin ’ya’yansa sun yi garkuwa da shi ko sun tilasta masa sayar da kadarorinsa.

“Yarana ’ya’yan albarka ne, babu wanda ya musguna min ko ya sace ni."

Ya bayyana takaicinsa kan matakin da suka ɗauka, yana cewa bai san wani laifi da ya yi musu ba.

“Na haife su, na raine su, na biya musu kuɗin makaranta, duk inda suka ce za su yi karatu sun yi. Ban san laifin da na yi musu ba.”

Kara karanta wannan

2027: Kawu Sumaila ya fadi zabinsa daga cikin masu son takarar gwamna a Kano

Alhaji Isma’ila ya jaddada cewa dukiyar tasa ce, kuma yana da ’yancin yin duk abin da ya ga dama da ita. Ya kuma yi gargaɗin cewa idan rikicin bai tsaya ba, zai miƙa al’amarin ga Allah.

Ya yi ikirarin cewa zai iya tsinewa yaran da suke naman hana shi kwanciyar hankali a kan dukiyarsa a karshen rayuwarsa.

An kama mugun 'dan daba a Kano

A baya, mun wallafa cewa rundunar ’yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke Abba Aliyu Fiya, wani matashi mai shekaru 26 da aka dade ana nema ruwa a jallo, bisa zargin jagorantar ayyukan daba.

A hirarsa da rundunar, Abba Fiya ya bayyana cewa ya yi fadan daba da kashe-kashe a jihohin Kano, Legas da Ribas (Fatakwal), lamarin da ya sake tayar da hankali kan matsalar daba a manyan biranen Najeriya.

Abba Fiya ya amsa cewa ya shafe kusan shekaru bakwai yana cikin harkar daba, inda ya bayyana cewa rikice-rikicen daba da suke yi kan kai ga mutuwar mutane, ko dai a wurin artabu ko kuma bayan an watse.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng