Bahaushe Ya Sha Ruwan Yabo bayan Mayar da Wayar iPhone da Ya Tsinta a Kasuwa

Bahaushe Ya Sha Ruwan Yabo bayan Mayar da Wayar iPhone da Ya Tsinta a Kasuwa

  • Wata mata ta bayyana yadda wani mutumin Arewa ya dawo mata da wayarta ta iPhone da ta ɓata lokacin sauka daga keke Napep
  • Matashin ya gano wayar a titi, ya biyo hanya har ya same ta a wajen aikinta, sannan ya ba ta damar kira don tabbatar da cewa wayarta ce
  • Dangin matar da mutanen da ke kusa sun yi masa addu’a, yayin da matar ta yaba da gaskiyarsa tare da cewa har yanzu mutane nagari suna nan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

An kwarara yabo ga wani dan Arewa bayan mayar da wayar da ya tsinta mai tsadar gaske ga wata mata a kasuwa.

Matar ta ruwaito yadda wani mutumin da ake ganin Bahaushe ne ya mayar mata da wayar iPhone da ta ɓata yayin sauka daga keke a kasuwa.

Kara karanta wannan

'Ka nemi kashe ni,' Wike ya yi martani mai zafi ga Buratai bayan rigima da soja

Bahaushe ya mayar da wayar Iphone da ya samu a kasuwa
Matashin da ya mayar da wayar Iphone yayin da ake murna a cikin kasuwa. Hoto: SPRING FOODS.
Source: TikTok

Yadda Bahaushe ya farantawa mata rai a kasuwa

A bidiyon TikTok, da SPRING FOODS ya wallafa, matar ta ce mutumin ya tarar da wayar a hanya ya bi sawunta har wurin da take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tambaye ta ko ta rasa wani abu, kuma lokacin ta bincika, sai ta ga wayar ba ta cikin jaka.

Ya bukace ta ta kira layinta, kuma wayar ta yi ƙara a aljihunsa, nan take kuwa ya miƙa mata wayar, mutanen wurin sun yi masa addu’a bisa halin kirki.

Matar ta gode sosai, tana cewa lamarin ya nuna akwai mutane nagari har yanzu, ta roƙi Allah ya saka wa mutumin alheri, tana mai godewa Ubangiji bisa taimakonsa.

A cikin kalamanta, matar ta ce:

“Da ya iso wurina, sai ya tambaye ni ko na ɓata wani abu, da farko na rikice. Na duba jakata ban ga iPhone ɗina ba.

Kara karanta wannan

Matar shugaban APC ta fara gangamin tazarcen Tinubu, ta yi kira ga matan Najeriya

"Sai ya ce in kira layina, kuma da na kira, wayar ta yi ƙara cikin aljihunsa. Nan take ya miƙa min wayar.”
An yabawa dan Arewa bayan dawo da wayar da ya tsinta
Matashin ya farantawa mata rai a kasuwa bayan dawo da wayar iPhone. Hoto: SPRNG FOOD.
Source: TikTok

Abin da mutane ke cewa kan lamarin

Wannan lamari ya farantawa mutane da dama rai inda wasu ke mamakin irin gaskiya da matashin ya nuna duk da halin matsin tattalin arziki da ake ciki.

Ba a dai fadi inda lamarin ya faru ba ko kuma jihar da kasuwar da abin ya afku amma ya nuna karara daga yankin Kudancin Najeriya ne.

Wasu sun yi martani game da lamarin.

Selected:

"Ina ga yan Arewa sun fi kowa farin ciki a wannan mako, Laftanar Yerima, Aboki."

Jamee:

"Wannan shi ne abin da makiyan Najeriya ba su son kowa ya gani."

Ammascco:

"Wannan shi ne yadda muke a baya, kafin gurbatattun shugabanni su raba mu kan siyasarsu."

Direban Keke Napep ya tsinci jakar kudi

A baya, mun ba ku labarin cewa rundunar 'yan sandan Kano ta yaba da tsantsar gaskiya da rikon amana da wani direban adaidaita sahu ya nuna a jihar.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun dura a Rivers? Fadar shugaban kasa ta magantu

Matashin mai suna Safiyanu Mohammed ya mika wata jaka makare da kudi da ya tsinta a kwanar dakata ga rundunar 'yan sanda.

Jam'in hulda da jama'a na rundunar a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an mika cigiyar mai jakar a lokacin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.