Sanadiyyar Rasuwar Sarkin Gusau da Gwagwarmayar da Ya Yi a Rayuwar Shi

Sanadiyyar Rasuwar Sarkin Gusau da Gwagwarmayar da Ya Yi a Rayuwar Shi

  • A yau Sarkin Gusau, Dr Ibrahim Bello ya rasu yana da shekara 71 bayan fama da doguwar rashin lafiya a Abuja
  • Binciken Legit ya gano cewa Sarkin ya hau karagar mulki a 2015 kuma ya yi aiki da hukumomin lafiya da ilimi kafin sarauta
  • Marigayin ya taba zama Kwamishina, Darakta Janar da Sakatare a masarautar kafin zama Sarki shekara 10 da ta wuce

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana alhinin sa kan rasuwar mai martaba Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu da safiyar Juma’a a birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya bayyana Sarkin a matsayin uba mai bada goyon baya da shugaba nagari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kyautata jihar Zamfara da al’umarta.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta jijjiga Arewa, Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau ya rasu

Marigayi Sarkin Gusau, Dr Ibrahim Bello
Marigayi Sarkin Gusau, Dr Ibrahim Bello. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

Hadimin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya wallafa a Facebook cewa Dauda Lawal ya samu labarin rasuwar cikin bakin ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da marigayi Sarkin Gusau.

Shafe shekaru 10 a matsayin Sarkin Gusau

Marigayi Dr Ibrahim Bello ya hau karagar mulki a ranar 16 ga Maris, 2015, inda ya zama Sarkin Gusau na 15.

An ce, a cikin shekara 10 na mulkinsa, ya kasance Sarki mai kishin al’umma, da sadaukarwa da kuma jajircewa.

Aikin gwamnati kafin zama sarki a 2015

Kafin ya zama sarki, marigayin ya shahara a aikin gwamnati, inda ya fara aiki da asibitin Gusau a 1977 bayan kammala karatu a makarantar jinya.

A wata hira da yi da jaridar Punch a 2018, marigayin ya ce ya koyar a makarantar jinya a Sokoto daga 1985 zuwa 1986.

A bangaren karatu, Sarkin ya ce ya samu takardar diloma a fannin koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano a 1987, kafin ya tafi Jami’ar Manchester a Ingila inda ya samu digiri na biyu a fannin lafiya.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Gwamna ya ji ba daɗi, hadiminsa kuma tsohon ɗan majalisa ya rasu

Sauran ayyukan da Sarkin Gusau ya yi

Bayan dawowarsa daga Ingila, Sarkin ya bayyana cewa ya ci gaba da koyarwa kafin a ba shi wani aiki a fannin lafiya.

Daga nan ya rike mukamai daban-daban a Sakoto, Jega da Gwadabawa kafin ya zama darakta a cibiyar kiwon lafiya ta Zamfara.

Daga nan aka ɗaga shi zuwa babban darakta a Ma’aikatar Lafiya, daga bisani kuma ya zama Kwamishina a Ma’aikatar Lafiyar Dabbobi.

Sakamakon kwarewarsa da amana, an nada shi Darakta Janar kuma daga baya ya zama Sakatare a masarautar Gusau.

Jinya ta yi sanadin rasuwar Sarkin Gusau

Bayan rasuwar dan uwansa, ya shiga sahun masu neman gadon sarauta kuma tare da goyon bayan jama’a da iyalai, Allah ya ba shi nasara inda ya hau sarauta a 2015.

Dr. Ibrahim Bello ya bar duniya yana da shekaru 71 a duniya, ya rasu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya a Abuja.

Marigayin ya kasance ɗan gidan sarauta na Sambo Dan Ashafa kuma an haife shi a Wonaka a 1954.

Kara karanta wannan

'Ya yi mani albishir zan yi tazarce,' Tinubu ya fadi wanda ya taimaka ya zama shugaban kasa

Gwamnan Zamfara ya yi jimamin rasuwar Sarkin Gusau
Gwamnan Zamfara ya yi jimamin rasuwar Sarkin Gusau. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

Sarkin Musulmi ya je taro kasar Ingila

A wani rahoton, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya halarci wani taron addini a kasar Igila a makon da ya wuce.

Taron ya samu halartar shugabannin duniya daga kasashe daban daban kuma Sarkin Ingila, Charles III ma ya hallara.

A yayin taron, Sultan ya yi kira na musamman kan hada kai wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng