Sun Kwanta Dama: Buhari, Dantata da Wasu Manyan Ƴan Najeriya da Suka Rasu a 2025

Sun Kwanta Dama: Buhari, Dantata da Wasu Manyan Ƴan Najeriya da Suka Rasu a 2025

  • A shekarar 2025, Najeriya ta yi babban rashi na manyan mutane suka taka rawar gani a siyasa, kasuwanci, ilimi da sarauta
  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, da attajirin mai kudi Aminu Dantata, na daga cikin wadanda suka riga mu gidan gaskiya
  • Legit Hausa ta jero fitattun mutane biyar da suka rasu a tsakanin watan Yuni da Yulin 2025, ciki har da Sarki Sikiru Adetona na kasar Ijebu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A tsakanin Yuni da Yulin 2025, Najeriya ta yi babban rashi na wasu fitattun mutane da suka taka rawa a siyasa, tattalin arziki, al’adu, da kuma harkokin ilimi.

Cikin wadanda suka riga mu gidan gaskiya akwai tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, mashahurin attajiri kuma ɗan kasuwa, Aminu Alhassan Dantata.

Daga farkon Yuni zuwa Yulin 2025, Najeriya ta rasa wasu fitattun mutane, ciki har da Buhari da Dantata
Marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata | Marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Haka nan akwai sarakunan gargajiya, masana da fitattun ‘yan Najeriya da suka bar tarihi mai ɗaukar hankali da ya sanya jama’a cikin alhini a ciki da wajen ƙasa.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Buhari ya tsira bayan yunkurin kashe shi a 2014

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan rahoton, Legit Hausa ta jero manyan mutanen da suka rasu a tsakanin Yuni da Yulin 2025:

1. Muhammadu Buhari

A ranar 13 ga Yuli, 2025, muka ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu yana da shekara 82 a wani asibitin London inda yake jinya.

Buhari, wanda aka haife shi a 1942 a garin Daura, jihar Katsina, ya shugabanci Najeriya a mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, inda ya yi kaurin suna da kan dokoki masu tsauri.

A 2015, ya dawo kan mulki a tsarin dimokuradiyya bayan lashe zabe a karkashin jam'iyyar APC, karon farko da aka kayar da jam’iyya mai mulki a tarihin Najeriya.

Duk da ya shahara da yaki da cin hanci da kuma Boko Haram, matsalolin tattalin arziki da tarzomar #EndSARS, canja fasalin kudi, da sauransu sun jawo wa gwamnatinsa suka.

2. Aminu Alhassan Dantata

A ranar 28 ga Yuni, 2025, Legit Hausa ta ruwaito cewa attajiri Aminu Alhassan Dantata ya rasu yana da shekara 94 a duniya.

Kara karanta wannan

An dage jana'izar marigayi shugaba Buhari, an saka sabon lokaci

Dantata, wanda aka haife shi a 1931 a Kano, ya gaji harkar kasuwanci daga mahaifinsa kuma ya bunƙasa ta ta hanyar jagorantar kamfanin Dantata & Sawoe da kuma kasancewa darakta a rukunin kamfanonin Dangote.

Ya taka muhimmiyar rawa a gine-gine, noma da banki, ciki har da kafa bankin Musulunci na Jaiz, wanda ya taimaka wajen karfafa tattalin arzikin Najeriya.

Ayyukan sa na agaji da taimako a fannin ilimi da walwalar jama’a sun sanya shi cikin waɗanda ake girmamawa ƙwarai a kasar nan.

3. Farfesa Jibril Aminu

A ranar 5 ga Yuni, 2025, Farfesa Jibril Aminu, masanin lafiyar zuciya kuma mai fada a ji a harkar siyasa, ya rasu a Abuja yana da shekara 85 bayan fama da jinya.

Wanda aka haife shi a 1939 a jihar Adamawa, Farfesa Jibrin ya kammala digiri na likitanci a jami’ar Ibadan a 1965 sannan ya samu digiri na gaba a London a 1972.

Ya zama sakataren hukumar NUC na farko daga 1975 zuwa 1979, sannan ya shugabanci jami’ar Maiduguri daga 1980 zuwa 1985.

Ya kuma kasance ministan ilimi da na man fetur daga 1989 zuwa 1992, sannan sanata daga 2003 zuwa 2011, inda ya jagoranci sauye-sauye da dama.

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari ta taɓa Ndume, ya faɗi wasu abubuwa da ya sani

Mataimakin shugaban kasa Shettima ya bayyana shi a matsayin "shugaban da ba a samun irinsa sau biyu" a lokacin jana’izarsa da aka yi a Abuja.

Oba Sikiru Adetona, sarkin kasar Ijebu ya rasu a ranar Lahadi, awanni kadan bayan rasuwar Buhari
Sarkin kasar Ijebu da ke jihar Ogun, Oba Sikiru Kayode Adetona ya rasu a ranar Lahadi, 14 ga Yulin 2025. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: UGC

4. Oba Sikiru Kayode Adetona

Oba Sikiru Adetona, wanda ya zama Awujale na masarautar Ijebu tun 1960, ya kasance daya daga cikin sarakunan da suka dade suna mulki a Najeriya.

Ya shahara wajen kare al’adun Yarbawa da kuma inganta ilimi da ci gaba a yankinsa. Rasuwarsa ta bar gibi a masarautar Ijebu da al’ummar Yarbawa gaba ɗaya.

Mun ruwaito cewa mai martaba sarkin ƙasar Ijebu, Oba Sikiru Kayode Adetona, ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

5. Oba Owolabi Olakulehin

Legit Hausa ta ruwaito cewa Oba Olakulehin ya zama Olubadan na Ibadan tun shekarar 2024, kuma ya rasu ne a a ranar Litinin, 7 ga watan Yulin 2025.

Kodayake bai daɗe a kan karagar mulki ba, ya taka rawar gani a matsayin dattijo mai kishin ci gaban garin Ibadan.

Olakulehin ya karɓi sandar mulki daga gwamnan Oyo, Seyi Makinde, a Yulin 2024, inda ya zama sarkin Ibadan na 43, kuma ya rasu yana da shekaru 90.

Kara karanta wannan

IBB ya tura sakon jaje ga Aisha Buhari, ya fadi alakarsa da mijinta da ya rasu

Tinubu ya dauki matakai bayan rasuwar Buhari

A wani labarin, mun ruwaito cewa, bayan rasuwar Muhammadu Buhari, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki wasu muhimman matakai biyar domin girmama marigayin.

Buhari, wanda ya mulki Najeriya a matsayin shugaban soja daga 1984 zuwa 1985, ya dawo mulki a 2015 a matsayin shugaban farar hula har zuwa 2023.

Daga cikin matakan da Tinubu ya dauka har da umarnin a saukar da tutoci na kwana bakwai, yayin da Kashim Shettima, zai jagoranci rakiyar gawar Buhari daga London zuwa gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com