Bayan Dusten Tanshi, Pantami Ya Sanar da Rasuwar Babban Malamin Musulunci

Bayan Dusten Tanshi, Pantami Ya Sanar da Rasuwar Babban Malamin Musulunci

  • Rahotanni na nuni da cewa malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Yahya Harun Gombe ya rasu a safiyar yau Litinin
  • Malamin ya kasance shugaban daliban Jami'ar Musulunci ta Madina na Gombe, kuma ma’aikaci ne a hukumar alhazai ta jihar
  • Biyo bayan labarin rasuwarsa, mutane da dama sun bayyana irin kyakkyawan halinsa tare da yi masa addu’ar samun rahamar Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - An shiga jimamin rasuwar Sheikh Yahya Harun Gombe, wanda aka fi sani da Malam Yahya Ci Rabonka, wanda ya rasu a safiyar Litinin, 7 ga Afrilu, 2025.

An yi jana'izarsa Malamin da misalin karfe 10:00 na safe a barikin ‘yan sanda da ke cikin birnin Gombe.

Pantami
Pantami ya yi jimamin rasuwar malamin Musulunci a jihar Gombe. Hoto: Professor Isa Ali Pantami|Abdullahi Yakubu Dauda
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan rasuwar malamin ne a cikin wani sako da Sheikh Isa Ali Pantami ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Atiku da shugaban SDP sun ziyarci Aisha Buhari bayan an mata rashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin musulunci, Umar Shehu Zariya ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Yahya Harun a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Marigayin ya kasance daya daga cikin manyan daliban Jami’ar Madina da suka dawo gida suka ci gaba da koyar da ilimi, kuma ma’aikaci ne a hukumar alhazai ta jihar Gombe.

Sheikh Pantami ya yi ta'aziyyar Yahya Harun

Sheikh Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar malamin, inda ya ce yana cikin manyan malamai a jihar Gombe.

Pantami ya wallafa a cewa:

"Muna mika ta'aziyyar rasuwar daya daga cikin aminanmu kuma manyan malamai a Jihar Gombe, Yahya Harun. Wanda shi ne shugaban daliban jami'ar Madina 'yan jihar Gombe.
"Muna kara ta'aziyya zuwa ga iyalansa da aminansa da dalibansa, da yan'uwansa da dukkan jama'ar da rasuwar wannan dan'uwa ta shafe su."

Bayanan wasu daga cikin dalibansa

Abdullahi Yakubu Dauda ya bayyana Sheikh Yahya a matsayin mutum nagari, wanda ya yi karatu a farkon lokutan bude Jami’atul Islamiyya.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 19 sun yi maganar rasuwar babban malami, Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Abdullahi Yakubu Dauda ya wallafa a Facebook cewa:

“Na samu damar yin karatu da shi a wasu lokuta daban-daban. Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa.”

A yayin tattaunawa da Legit, Ahmad Muhammad ya ce malamin ya kasance mutum ne mai hakuri da jajircewa.

"Ina tuna lokacin da muka yi daurar daliban jami'ar Madina a makarantar Abubakar Sadiq, yana cikin masu kokarin ganin komai ya tafi yadda ya kamata."

Shi ma Kaleemullah Ahmad Hinna ya bayyana rasuwar malamin da cike da alhini, yana mai cewa ya kasance limami a masallacin barikin ‘yan sanda da kuma mutum mai son sada zumunci.

Kaleemullah ya wallafa a Facebook cewa:

“Ranar Juma’a da ta gabata muna tare da shi, har muka yi barkwanci. Shi Boboli, ni kuma Bateri. Mutum ne mai fara’a da kyakkyawar mu’amala.”

Kaleemullah ya roki al’umma da su saka marigayin cikin addu’o’insu, yana mai fatan Allah ya karbi ayyukansa da sa shi cikin Aljannah Firdaus.

Kara karanta wannan

Yadda Dutsen Tanshi ya dawo Najeriya daga Indiya duk da tsananin rashin lafiya

Addu’o’i sun karade kafafen sada zumunta

Mutane da dama sun bayyana alhinin su bisa wannan rashi da ya girgiza jama’a, tare da wallafa hotuna da addu’o’i a dandalin sada zumunta.

Dukkanin su sun yi tarayya wajen bayyana yadda marigayin ya kasance mutum mai saukin kai da hidima ga al’umma.

Umar Shehu
Umar Shehu Zariya ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Yahya Harun. Hoto: Mika'il Abuubakar YYG
Asali: Facebook

Yusuf Sambo ya yi kiran haduwar Izala

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar malaman kungiyar Izala, Sheikh Yusuf Sambo ya yi kira da sake haduwar kungiyar.

A nasa bangaren, Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yaba wa Yusuf Sambo kan kiran da ya yi game da haduwar kungiyar.

Sai dai wasu 'yan kungiyar na ganin cewa ba haduwa ya kamata a fara ba, suna ganin ya kamata dawo mu'amala mai kyau ne a karon farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng