Abin da Sheikh Bala Lau Ya Fada bayan Rasuwar Dr Idris Dutsen Tanshi

Abin da Sheikh Bala Lau Ya Fada bayan Rasuwar Dr Idris Dutsen Tanshi

  • Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau, ya miƙa ta’aziyya bisa rasuwar Sheikh Idris Abdul’azeez Dutsen Tanshi
  • Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi addu’a ga marigayin tare da rokon Allah Ya gafarta masa kurakuransa
  • Biyo bayan rasuwar Dr Idris, mutane da dama sun yi ta bayyana alhinin su tare da yin addu’a ga malamin addinin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Shugaban ƙungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya miƙa saƙon ta'aziyya ga dangi da iyalan marigayi Sheikh Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi.

Shehun Malami, Dr Idris Dutsen Tanshi ya rasu a jihar Bauchi a daren Juma’a, kuma za a masa janaza ne a jihar.

Bala Lau
Sheikh Bala Lau ya yi ta'aziyyar rasuwar Dr Idris Dutsen Tanshi. Hoto: Jibwis Nigeria|Dutsen Tanshi Majlis Bauchi
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin saƙon ta’aziyyarsa, Sheikh Bala Lau ya bayyana mutuwar marigayin a matsayin babban rashi ga Ahlussunnah da al’ummar Musulmi gaba ɗaya.

Baya ga haka, ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa Ya kuma sa Aljanna ce makomarsa.

Bala Lau ya yi ta'aziyyar Idris Dutsen Tanshi

Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa mutuwa rigar kowa ce, don haka ya roƙi Allah da Ya jikan Sheikh Idris Dutsen Tanshi da rahama Ya sanya haske a kabarinsa.

"Allah ka gafarta masa kurakuransa, ka sanya Aljannah ce makomarsa, ka kyautata bayansa, ka bawa iyalansa dangana,"

- Sheikh Abdullahi Bala Lau

Ya ƙara da cewa marigayin ya yi ayyuka masu yawa na hidima ga addini da koyar da Sunnah, don haka ya dace a ci gaba da yi masa addu’a da neman rahama daga Allah.

Pantami
Sheikh Pantami ya yi ta'aziyyar Dr Idris Dutsen Tanshi. Hoto: Professor Isa Ali Pantami|Dutsen Tanshi Majlis
Asali: Facebook

An yi jimamin rasuwar Dr Idris Dutsen Tanshi

Bayan ta'aziyyar Sheikh Abdullahi Bala Lau, mutane da dama sun bayyana alhininsu tare da yi masa addu’a.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Idris Dutsen Tanshi ya fada kan rashin lafiya da mutuwa kafin ya Cika

Fatima Haruna ta ce:

“Wannan dare zai kasance mafi muni a wajen duk wani Ahlussunnah, amma ku sani cewa mutuwar malam ba za ta sa a daina ruguza bidi’a da shirka ba.
"Allah zai kawo wanda ya fi shi.”

Engr Abdullahi Baban Bajo ya ce:

“Ubangiji Allah Ya jikan sa da rahama, yasa jinyar da yayi ta zama kaffara ga dukkan zunubansa.”

Sarkin Malaman Galadima Ward ya yi addu’a da cewa:

“Ya Allah, muna roƙon ka da sunayen ka kyawawa da siffofin ka Maɗaukaka ka jikan Malam da rahama, ka sada shi da rahamarka.
"Malam yayi wa addinin ka hidima da Sunnah, ka ba shi lada a inda yayi daidai, ka gafarta masa inda yayi kuskure.”

Rasuwar Dr Idris Dutsen Tanshi ta girgiza al’ummar musulmi, musamman mabiyan Sunnah, tare da barin babban gibi a fagen ilimi da wa’azi.

Kara karanta wannan

'Ya na da zuhudu': Shaidar da mutane suka yi wa marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi

Wasiyoyi 5 da Dr Idris Dutsen Tanshi ya bari

A wani rahoton, kun ji cewa Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi ya yi wasiyoyi da dama kafin Allah ya masa rasuwa.

Sheikh Dr Idris ya bukaci al'umma da su kiyaye daukar hoto ya yi da za a masa sallar janaza ko kai shi makabarta.

Haka zalika daga cikin wasiyoyin da malamin ya yi ya gargadi al'umma da kaucewa yin zaman makoki bayan rasuwarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng