Wasiyoyi 5 da Marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi Ya Bari kafin Mutuwarsa
- An samu rahotanni kan wasiyoyin marigayi Dr. Idris Dutsen Tanshi, inda daga ciki ya bukaci a kiyaye wasu ka’idoji yayin jana’izarsa
- Rasuwar malamin ta girgiza al'umma a fadin Najeriya kuma tuni malamai da daliban ilimi sun fara aika sakonnin ta’aziyya ga iyalansa
- Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya yi karatu a Jami’ar Musulunci ta Madinah da Sudan, inda ya samu digiri da digirgir a fannin shari’a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi, rasuwa.
Dr. Idris, wanda ya yi karatu a Jami’ar Musulunci ta Madinah a fannin Shari’ar Musulunci, ya kuma samu digirin digirgir a fannin fikihu a Sudan, ya bar wasu wasiyoyi wa al'umma.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan wasiyoyin ne a cikin wani sako da shafin Dutsen Tanshi Majlis Bauchi ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamai da dalibansa sun fara aikawa da sakonnin ta’aziyya, suna rokon Allah Ya gafarta masa, Ya sa Aljannah ce makomarsa.
Wasiyyoyin marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi
A cewar wasiyyoyin da ya barwa iyalansa da dalibansa, marigayin ya bukaci a kiyaye wadannan abubuwa:
1. Bai yarda a dauki hotuna yayin jana’izarsa ba.
2. Bai yarda da yin zaman makoki ba.
3. Ya hana yin turereniya wajen daukar gawarsa.
4. Ya hana shiga makabarta da takalmi a lokacin birne shi
5. Ya ce kar a rika yada hotunansa bayan rasuwarsa.
Marigayin ya bukaci al’umma da su kiyaye wadannan abubuwa yayin jana’izarsa, yana mai rokon Allah Ya yafe masa kura-kurensa.
Malamai da dalibai sun fara aika ta’aziyya

Kara karanta wannan
"Yana da abin al'ajabi da kura kurai," Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan Dutsen Tanshi
Daga cikin malaman da suka aika sakon ta’aziyya akwai Sheikh Isa Ali Pantami da Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe.
Sheikh Isa Ali Pantami ya wallafa a Facebook cewa:
"Muna mika ta’aziyyar rasuwar Dr. Idris Abdulazeez zuwa ga iyalansa da yan’uwansa.
"Allah Ya yafe masa kura-kurensa, Ya sa Aljannah ce makoma. Allah Ya kyautata namu bayan na su."

Asali: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Sheikh Kabiru Gombe ya yi addu’a da cewa:
"Allah Ka jikan Dr. Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi, Ka kyautata makwancinsa, Ka haɗa mu da shi a gidan Aljannah Firdausi.
"Allah Ka kai haske kabarinsa, Ka gafarta masa kura-kurensa, Ka sanya Aljannah ce makomarsa, Ka kyautata bayansa, Ka ba wa iyalansa dangana. Ameen."
Tarihin karatun Dr Idris Dutsen Tanshi
Marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi ya fara karatun digiri a fannin Shari’ar Musulunci a Jami’ar Musulunci ta Madinah.
Daily Nigerian ta wallafa cewa ya ci gaba da karatunsa a Sudan, inda ya samu digirin digirgir a fannin Fikihu.
Legit ta tattauna Ibrahim Aminu
Wani mazaunin jihar Bauchi, Ibrahim Aminu Ilela da ya halarci makabarta yayin birne Dr Idris ya bayyana wa Legit cewa an yi kokarin kiyaye wasiyar da malamin ya yi.
"Ban halarci jana'izar ba, amma na je makabarta. Sheikh Guruntum da Dr Disina sun ta tunatar da mutane kan kiyaye wasiyar da ya yi.
"An yi amfani da jami'an tsaro wajen tabbatar da cewa mutane ba su shiga makabarta da takalmi ba kamar yadda ya bukata, sai dai abin da ba za a rasa ba."
Tabbas, Malam Idris ya kasance mutum mai kima da daukaka a tsakanin malaman Najeriya, duk da fama da ya yi da wasu malamai saboda bambancin ra'ayoyi.
Sai dai, sabani dai ba sabon abu bane a tsakanin malami, amma Malam Idris ya taba zaman kurkuku saboda wasu kalamai da ya yi da suka saba da abinda wasu malamai ke kai.

Kara karanta wannan
"Mutane sun manta": Tinubu ya faɗi aikin da Sheikh Dutsen Tanshi ya yi wa Najeriya
Hakazalika, ya kasance abokin musayar miyau da gwamnatin jihar Bauchi, inda ya bayyana rashin amincewarsa ga wasu ayyukan gwamnatin.
An kashe dan agajin Izala a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda da ba a gano su waye ba sun kai hari gidan wani dan agajin Izala a Abuja.
'Yan ta'addan sun kai hari ne har gidan dan agajin kuma suka hallaka shi ta hanyar sassara shi da makami.
Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi Allah wadai da kisan tare da kira ga jami'an tsaro su dauki mataki.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.
Asali: Legit.ng