Kwana Ya Kare: Malamin da Ya Karantar da Sheikh Kabiru Gombe Ya Rasu
- Sakataren kungiyar Izala na kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya sanar da rasuwar wani babban malaminsa, Ibrahim Bawa Gwani
- Malam Ibrahim Bawa Gwani ya kasance malami kuma tsohon shugaban makarantar jeka-ka-dawo ta Comprehensive da ke jihar Gombe
- Bayan ya rasu yana da shekaru 70, an gudanar da jana'izarsa a filin Idi na Sarkin Gombe da misalin ƙarfe 11:00 na ranar Laraba, 2 ga Afrilu, 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Allah ya yi wa Malam Ibrahim Bawa Gwani, tsohon Shugaban makarantar sakandirin jeka-ka-dawo ta Comprehensive a Gombe rasuwa yana da shekaru 70.
Sakataren kungiyar Izala na kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya yi jimamin rasuwar malamin.

Asali: Facebook
Sheikh Kabiru Gombe ya rasa malami
Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana cewa Malam Bawa Gwani na cikin malaman da suka ba shi gudumawa a harkar ilimin boko a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
"An yi rashi," Shugaba Tinubu ya yi magana da Allah ya karɓi rayuwar Galadiman Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kabiru Gombe ya ce marigayin ya rasu ya bar mata da 'ya'ya 12 da jikoki da dama a cikin shekaru 70 da ya yi a duniya.
Tuni dai aka gudanar da jana’izarsa a filin Idi na Sarkin Gombe, kusa da babbar kasuwar Gombe, da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar Laraba, 02 ga Afrilun 2025.
Shahararrun malamai, ciki har da Sheikh Isa Ali Pantami, sun bayyana alhinin su kan wannan babban rashi, suna mai addu’ar Allah ya jikansa.
Gudunmuwar marigayin a harkar ilimi
Malam Ibrahim Bawa Gwani ya kasance fitaccen malami da ya bayar da gudunmuwa a fannin ilimi a Jihar Gombe.
Sheikh Kabiru Gombe ya ce Malam Bawa Gwani ya shugabanci makarantar Comprehensive daga shekarar 1984 zuwa 1989.
Malam Bawa Gwani ya koyar da ɗalibai da dama waɗanda suka zama manyan mutane a fannonin rayuwa daban-daban.
Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, wanda shi ma ya kasance ɗaya daga cikin daliban marigayin, ya bayyana cewa ya taimaka masa kwarai wajen karatun Boko.

Kara karanta wannan
Abin da Buhari ya ce bayan rasuwar dattijo, Galadiman Kano, ya fadi giɓin da ya bari
Sheikh Pantami ya yi ta’aziyya
Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya bayyana rasuwar Malam Ibrahim Bawa Gwani a matsayin babban rashi ga al'umma.
A cikin sakon ta’aziyyar da ya wallafa a Facebook, Pantami ya ce:
"Muna mika ta'aziyyar rasuwar Alhaji Ibrahim Bawa Gwani zuwa ga iyalansa, da yayansa da yan'uwansa da dukkan al'ummah.
"Lallai wannan rashi ne mai girma. Allah Ya sa Aljannah ce makomarsa tare da iyayenmu da malamanmu da yan'uwanmu. Allah Ya kyautata na mu bayan na su."

Asali: Facebook
Addu’o’in alheri ga marigayin
Biyo bayan rubutun da Sheikh Kabiru da Pantami suka yi kan rasuwarsa, mutane da dama sun yi wa Bawa Gwani addu'a.
Al’umma sun yi ta’aziyya da addu’a ga iyalan sa, suna mai fatan Allah ya gafarta masa, ya sanya shi cikin rahamarsa, tare da sauran bayin Allah da suka riga mu gidan gaskiya.
Sheikh Jingir ya yi wa Dan Bello raddi
A wani rahoton, kun ji cewa, Shugaban malaman kungiyar Izala, Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya yi raddi wa Dan Bello.
Sheikh Jingir ya yi wa Dan Bello Raddi ne bayan ya zargi Sheikh Abdullahi Bala Lau da karkatar da kudin kwangila a wasu makarantu.
Asali: Legit.ng