'Ya'yan Abacha Sun Yi Martani bayan IBB Ya Yi Maganganu kan Mahaifinsu

'Ya'yan Abacha Sun Yi Martani bayan IBB Ya Yi Maganganu kan Mahaifinsu

  • Sadiq Abacha ya kare mahaifinsa, marigayi Janar Sani Abacha, yana mai cewa tarihi zai tuna da gudunmawar da ya bayar
  • Dan tsohon shugaban kasar ya ce Janar Sani Abacha mutum ne da aka yi wa hassada kuma ya kasance shugaba nagari
  • Haka zalika, Gumsu Abacha ta yi martani kan lamarin tana mai cewa ya kamata mutane su ji tsoron Allah kan abin da suke fada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Da ga tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya fito fili yana kare mahaifinsa dangane da yadda wasu ke siffanta shi a tarihin siyasar kasar nan.

Sadiq S. Abacha ya bayyana cewa duk da sukar da ake yi wa mahaifinsa, tarihi zai tabbatar da cewa ya kasance shugaba nagari.

Kara karanta wannan

'Sun so kashe shi': IBB ya fadi makircin da Abacha ya shirya masa da MKO Abiola

Abacha
'Ya'yan Abacha sun yi martani bayan IBB ya wallafa littafi. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Dan tsohon shugaban kasar ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabinsa ya zo ne bayan kaddamar da wani littafi da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya rubuta, wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Sadiq Abacha ya kare mahaifinsa

A wani rubutu da ya wallafa, Sadiq Abacha ya bayyana cewa mahaifinsa ya kasance shugaba da aka yi wa hassada, amma duk da haka tarihi zai tuna da shi a matsayin jagora nagari.

Daily Trust ta wallafa cewa Sadiq ya rubuta cewa:

"Mutumin ne da ake yi wa hassada, amma tarihi zai zai tuna da alherinsa. A matsayina na ɗansa, ina alfahari da shi a yau.
"Lallai kai ne mutumin da suke fatan su zama kamarsa."

Sadiq ya kammala rubutunsa da karin maganar Hausa da ke cewa:

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda salon mulkin IBB ya saɓa da sauran shugabannin Najeriya

"Duk wanda yayi jifa a kasuwa…"

Littafin IBB ya haifar da ce-ce-ku-ce

Jawaban Sadiq Abacha sun zo ne bayan an kaddamar da littafin tarihin rayuwar IBB mai suna A Journey in Service.

A cikin littafin, Babangida ya bayyana cewa yana da nadamar soke zaben June 12, 1993, wanda ya bayyana cewa MKO Abiola ne ya lashe shi.

Sai dai Babangida ya ce dalilin soke zaben ba daga gare shi kadai ya fito ba, illa wata manufa ce da Abacha da mukarrabansa suka jagoranta, ba tare da saninsa ba.

Abacha dai ya karbi mulki daga hannun Babangida a 1993 bayan juyin mulkin da ya jagoranta, inda ya mulki Najeriya har zuwa karshen rasuwarsa a 1998.

Abiola
MKO Abiola da IBB ya ce ya lashe zabe a 1993. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: UGC

Martanin 'yar Sani Abacha kan lamarin

Baya ga rubutun Sadiq Abacha, ‘yar marigayin mai suna Gumsu Abacha, ta wallafa wani gajeren sako a shafin ta na X

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

A sakon nata, ta rubuta kalma daya kacal: "Weakling", wato "rauni" ko "maras tushe", wanda ake ganin martani ne kai tsaye ga bayanan da IBB ya yi kan mahaifinta.

Wannan sakon nata ya jawo ce-ce-ku-ce, inda mutane ke ta tsokaci kan yadda dangin Abacha ke kare mahaifinsu daga zarge-zargen da ake yi masa a tarihi.

A karshe Gumsu Abacha ta rubuwa cewa:

"Allah ba ya barci fa!! Muyi hattara da duniya wallahi."

IBB ya ce Abiola ya lashe zabe a 1993

A wani rahoton, kun ji cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana cewa MKO Abiola ne ya lashe zaben 1993.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a yayin taron kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa da aka gabatar a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng