Tinubu Ya ba da Mamaki da Ya Tono Wani Sirri tsakaninsa da IBB

Tinubu Ya ba da Mamaki da Ya Tono Wani Sirri tsakaninsa da IBB

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana yadda ya taɓa kalubalantar tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida
  • Bola Ahmed Tinubu ya ce Janar Babangida bai yi amfani da damar da ya samu don kafa tarihin dimokuraɗiyya a Najeriya ba
  • Tsohon shugaban mulkin sojan ya ce soke zaɓen 12 ga Yuni, 1993 da ya yi ya kasance ne domin kare muradun ƙasa ba son zuciya ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana yadda ya taɓa kalubalantar tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida kan soke zaɓen 12 ga Yuni, 1993.

Tinubu ya yi bayanin ne yayin taron ƙaddamar da littafin tarihin Babangida mai suna A Journey in Service, wanda aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yadda jiga jigan Najeriya suka tara Naira Biliyan 17 ga IBB a zama 1

IBB TInubu
Tinubu ya fadi yadda ya kalubalanci Tinubu a 1993. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Rahoton Channels Television ya nuna cewar Tinubu ya tunkari Janar Babangida kai tsaye da ya rika jinkirta rantsar da su bayan zabensu a matsayin Sanatoci a 1993.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kalubalanci Babangida

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa lokacin da aka zaɓe su a majalisa a shekarar 1992, tsohon shugaban mulkin sojan ya jinkirta rantsar da su ba tare da cikakken dalili ba.

Bola Tinubu ya ce:

"Na tunkare ka cewa kana da damar kafa tarihi a wancan lokacin, amma ka ƙi yin hakan. Me ya sa ba ka rantsar da mu ba? Me ya sa kake ta jinkirta rantsar da mu?"

A cewar Tinubu, lokacin da ya yi wannan magana, da yawa sun yi zaton zai shiga gidan yari saboda wannan tsayuwa da ya yi.

"Sun yi tunanin cewa zan ƙare a kurkuku. Amma bayan na yi wannan furuci, sai ka fito ka gaisa da ni da hannu. Wannan abu ba zan taɓa mantawa da shi ba,"

Kara karanta wannan

IBB ya yi fallasa kan zaben 1993 da aka rusa, ya fadi rawar da Buhari ya taka a baya

- Bola Tinubu

Rahotanni sun nuna cewa bayanin da shugaba Bola Tinubu ya yi ya janyo tafi daga mahalarta taron.

Tinubu ya jinjinawa Ibrahim Babangida

Duk da cewa ya kalubalanci tsohon shugaban, Tinubu ya yaba wa Babangida kan irin gudunmawar da ya bayar wajen gina ƙasa.

Bola Tinubu ya ce:

"Ba domin kai ba, mutane irin na ba za su shiga siyasa ba. Irin cigaban da ka kawo wajen tafiyar da siyasa ya ba mu damar shigarta."

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa Babangida na daga cikin shugabannin da suka ƙirƙiro tsarin kawo matasa masu ƙwazo cikin siyasa.

Bola Tinubu ya ce hakan ya ƙarfafa gwiwar matasan Najeriya da ba su dama su shiga harkokin jagoranci.

Bola Tinubu
Bola Tinubu na jawabi yayin kaddamar da littafin Janar IBB. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Dalilin soke zaɓen Abiola a 1993

A nasa jawabin, tsohon shugaban mulkin sojan ya sake bayyana dalilinsa na soke zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993, wanda marigayi Moshood Abiola ya lashe.

Kara karanta wannan

"Tinubu mutumin kirki ne, yana da niyya mai kyau," Babban malami ya yi wa mutane Nasiha

Babangida ya ce:

"Na yanke hukuncin ne domin kare muradun ƙasa."

Babangida ya yi mulkin Najeriya daga 1985 zuwa 1993, kuma yana daga cikin shugabannin da suka fi tasiri a tarihin siyasar ƙasar nan.

An tarawa IBB Naira biliyan 17.5

A wani rahoton, kun ji cewa manyan Najeriya da suka halarci kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa a Abuja.

Legit ta rahoto cewa manyan 'yan kasuwa irinsu Aliko Dangote, Abdulsamad Rabi'u da sauransu sun tara kudi har Naira biliyan 17.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng