Fitaccen Ɗan Wasan Kwaikwayo a Najeriya Ya Shiga Matsala, Ya Yi Asarar $3.1m

Fitaccen Ɗan Wasan Kwaikwayo a Najeriya Ya Shiga Matsala, Ya Yi Asarar $3.1m

  • Dan wasan barkwanci, Mark Angel ya ce ya fuskanci kalubale a shekarar 2024, inda ya rasa dukiyarsa da ta kai dala miliyan 3.7
  • Mark Angel ya ce addu’a, magani da gudunmawar da ya samu daga iyalansa ne suka ceci rayuwarsa daga tunanin kisan kai
  • Fitaccen mai barkwancin ya gode wa ubangiji da masoyansa da suka tsaya tare da shi a wannan mawuyacin lokaci na rayuwarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fitaccen dan wasan barkwanci na Najeriya, Mark Angel ya bayyana darussa da kalubalen da ya fuskanta a shekarar 2024.

A cewarsa, shekarar 2024 ta kasance mafi tsanani a rayuwarsa amma ta kuma zama shekarar da ta koya masu abubuwa da yawa.

Mark Angel ya yi magana kan asarar da ya tafka a shekarar 2024
Fitaccen dan wasan kwaikwayo Mark Angel ya tafka asarar $3.1m a shekarar 2024. Hoto: markangelcomedy
Asali: Instagram

Makar Angel ya tafka asarar $3.1m

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Mark Angel ya ce ya yi asarar kudi da suka kai dala miliyan 3.7 a harkar hada hadar kudin 'forex'.

Kara karanta wannan

Ta ku ta kare: Sojoji sun shirya tsaf za su ga karshen 'yan ta'addan Najeriya a 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta cewa:

“Shekarar 2024 ta fara ne kamar kowace shekara amma ban san cewa zan gamu da jarabawowi kala kala da za su canja rayuwata ba."

Ya kara da cewa ya rasa dukiyarsa gaba daya saboda yarda da mutanen da ba su cancanta ba, kuma babu wanda ya sani sai iyalinsa da 'yan uwansa.

Mark Angel ya kusa halaka kansa

Asarar ta kai shi ga shiga bashi mai yawa, inda ya rasa kadarorinsa daya bayan daya ga tarin mutane da kamfanonin da ke bin sa bashi.

Mark Angel ya bayyana cewa ya shiga mawuyacin hali har ya fara tunanin halaka kansa saboda mawuyacin halin da ya jefa rayuwarsa.

Sai dai tare da taimakon magani, addu’o’i da goyon bayan masoyansa, ya ce ya samu damar tsallake wannan mummunar jarabawar rayuwa.

Mark Angel ya godewa wasu makusantansa

Ya gode wa 'ya’yansa mata, Victoria da Mila da suka tunatar da shi amfanin rayuwa, da kuma tsohuwar matarsa Mandy da ta kawi masa dauki.

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood Radeeya Jibril ta yi aure, ta lissafa mutane 7 da suka taimaka mata

Haka zalika, ya gode wa abokansa, Blessing da Bright, wadanda suka tsaya tare da shi a lokacin tsanani da dadi ba tare da sun juya masa baya ba.

Mark ya kara bayyana cewa ya fuskanci wani rikici a 2024 wanda ya lalata ginshikin aikinsa kuma ya fito da rashin gaskiyar wasu daga cikin na kusa da shi.

Mark Angel ya gano makiya a abokansa

Duk da haka, ya ce ya dauki wannan darasi a matsayin dama ta gyara gabansa, inda ya kyale komai ga ubangiji domin kare shi da kara masa karfin zuciya.

Shahararren mai barkwancin ya ce:

“A cikin wannan rikicin, uabngiji ya fara bayyana gaskiya. Ya fallasa abokai da wasu makusanta na na karya da ke cin dunduniya ta."

Ya kara da cewa, duk da radadin cin amanar, hakan bai sare masa guiwa ba illa ma ya kara koyon darasi kan rayuwa da kuma zamantakewa.

Mark Angel ya jawo ce-ce-ku-ce a intanet

Kara karanta wannan

'Duk da amaryata ‘yar shekara 14 ta nemi kashe ni da guba, ina kaunarta' inji Ango

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan wasan barkwanci, Mark Angel, ya jawo cece-kuce kan wani bidiyo da aka gan shi yana taimakon wata mata daga motar alfarma.

Mark, wanda aka san shi da wasannin ban dariya tare da ‘yan tawagarsa kamar Emmanuela da Success, ya ba mabiyansa mamaki ganinsa cikin kayan alfarma yana taimako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.