'Duk da Amaryata ‘Yar Shekara 14 Ta Nemi Kashe Ni da Guba, Ina Kaunarta' Inji Ango

'Duk da Amaryata ‘Yar Shekara 14 Ta Nemi Kashe Ni da Guba, Ina Kaunarta' Inji Ango

  • Kamisu Haruna ya auri wata budurwa mai suna Zahra’u Dauda wanda ta kusa zama sanadiyyar ajalinsa
  • Amaryar ta jefa masa guba a cikin abinci amma duk da haka ya dage cewa ya na kaunar matarsa har gobe
  • Angon ya ce tsohon saurayin yarinyar mai shekara 14 ne ya yaudare ta ganin ba gama fahimtar rayuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Jigawa - Wani mutumi mai shekara 34 ya kwashe labarin yadda amaryarsa ta kusa aika shi barzahu ta hanyar jefa masa guba.

Kamisu Haruna mai shekara 34 ya gamu da jarrabawar rayuwa da amaryarsa ta sa masu guba a cikin abinci bayan an yi aurensu.

Aure.
Amarya ta kusa kashe ango da guba a abinci a Jigawa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar Premium Times ta yi hira da angon wanda yanzu haka amaryarsa ta aika abokinsa barzahu a sakamakon cin guba a abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanaki biyu da yin auren Kamisu Haruna da sahibarsa a garin Albasu da ke karamar hukumar Jahun a Jihawa, ya kusa mutuwa.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Sarki a Najeriya ya gamu mummunan hatsari, Allah ya yi masa rasuwa

Ango yana shirin tarewa da amarya

A ranar 20 ga watan Disamba 2024, angon ya dauki amaryarsa mai suna Zahra’u Dauda bayan an daura masu aure a Kiyawa a jihar Jigawa.

Jim kadan bayan jama’a sun watse sai Malama Zahra’u ta kawowa ango da abokansa - Muhammad Alpha and Isyaku Adamu, abinci.

Yadda aka sa guba a abincin ango

"Mun ga kawayenta suna zuwa wurin wani shago da ke kusa inda mu ke zaune. Suka zo da taliya da nama, suka ce amarya ta ce a kawo mana abinci.
"Lokacin da muke cin abinci, sai mu ka lura da dandanon wani sinadari sai mu ka daina cin abincin, mu na zargin cewa an sa guba a ciki.
"Daga nan sai mu ka fara jin ciwon ciki. Mun sha madara amma lamarin ya cigaba da yin muni, nan mu ka ruga asibiti.
A nan (asibiti) aka tabbatar da cewa abokinmu Muhammad Alpha ya rasu."

Kara karanta wannan

Amarya ta hada baki da tsohon saurayinta sun saka guba a abincin ango

- Kamisu Haruna

Sharrin tsohon sarurayin amarya ne

Duk da abin da ya faru, angon ya hakikance cewa amaryar ta na kaunarsa, ya zargi tsohon saurayinta da ba ta guba domin ta kashe shi.

Har gobe ya na kaunar matarsa, a cewarsa kaddara ce ta jawo Lawan Musa da ke Bagata Gabas Yamma ya ba amaryar gurguwar shawara.

Yayin da ake binciken lamarin, Hamisu ya ce ba auren dole aka yi masu ba, suna son junansu.

Faston da aka cafke ya kubuta

Bishof Godwin Okpala wani fasto a cocin angilikan a Najeriya ya hadu da sharrin 'yan bindiga kamar yadda muka kawo rahoto kwanan nan.

Amma a karshe addu'a ta yi tasiri, limamin cocin, Farfesa Godwin Okpala ya shaki iskar 'yanci bayan kusan wata guda a tsare da direbansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng