Kwana Ya Kare: Mahaifiyar Gwamnan Jigawa Ta Rasu, Ya Nemi Addu'a

Kwana Ya Kare: Mahaifiyar Gwamnan Jigawa Ta Rasu, Ya Nemi Addu'a

  • Gwamnan Jihar Jigawa watau Malam Umar Namadi, ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi Umar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa za a gudanar da jana’izar marigayiyar a yau da misalin karfe 4:30 na yamma a garin Kafin Hausa
  • Gwamna Namadi ya bukaci jama’a su yi addu’a domin Allah ya jikanta ya kuma ba su hakurin babban rashin da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - An shiga jimami a jihar Jigawa bayan rasuwar mahaifiyar gwamna Malam Umar Namadi.

Gwamnan ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi Umar, wacce ta rasu a safiyar Laraba, 25 ga Disamba, 2024.

Umar Namadi
Mahaifiyar gwamnan Jigawa ta rasu. Hoto: Garba Muhammad
Asali: Twitter

Legit ta gano rasuwar Hajiya Maryam ne a cikin wani sako da mai magana da yawun gwamnan, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Yaki da yunwa: Gwamna ya gayyato 'yan China domin koyar da noman zamani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An nemi yin addu'a ga mahaifiyar gwamna

Gwamna Namadi ya roki jama’a da su taya shi da iyalansa addu’a domin Allah ya gafarta wa marigayiyar ya kuma sanya ta cikin Aljannar Firdausi.

Bayan sanarwar rasuwar Hajiya Maryam, mutane da dama sun fara aikawa da sakonnin ta’aziyya ga gwamna da iyalansa, musamman a kafafen sada zumunta.

Rasuwar mahaifiyar gwamnan ta zo ne kasa da mako daya da aurar da 'yarsa, Dr Salma Umar Namadi a birnin Dutse.

Za a yi jana'izar mahaifiyar gwamna Namadi

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa gwamna Umar Namadi ya tabbatar da cewa a yau za a gudanar da jana’izar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam, bisa ga tsarin addinin Musulunci.

Garba Muhmmad ya kara da cewa jana’izar marigayiyar za ta kasance ne da misalin karfe 4:30 na rana.

Haka zalika, jana’izar za ta gudana a garin Kafin Hausa, mahaifarta, inda dubban jama’a za su halarta domin taya iyalanta jimamin wannan rashi.

Kara karanta wannan

An cafke jigon NNPP kan zargin sukar gwamna Zulum, ana fargabar kai shi kotu

Kanwar Janar Abdulasami Abubakar ta rasu

A wani rahoton, kun ji cewa Allah SWT ya yi kanwar tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar rasuwa kwanan nan.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sakon ta'aziyya ga Abdulsalami Abubakar kan rasuwar Hajiya Asabe, ya ce rashi ne babba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng