Yadda Gwamnonin Arewa 19 Suka Taya Buhari Murnar Cika Shekaru 82

Yadda Gwamnonin Arewa 19 Suka Taya Buhari Murnar Cika Shekaru 82

  • Shugaban Gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya shugaba Muhammadu Buhari murnar cika shekaru 82
  • Inuwa Yahaya ya bayyana Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba da ke cike da kishi, rikon amana, da jajircewa ga ci gaban Najeriya
  • Gwamnan ya ce gwamnonin Arewa 19 suna addu’ar Allah ya kara wa Buhari lafiya da hikima domin ci gaba da taimakawa Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Shugaban Gwamnonin Jihohin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta 82.

A cikin wani sakon taya murna da Inuwa Yahaya ya fitar a madadin gwamnonin Arewa 19, ya bayyana Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba.

Buhari
Gwamnonin Arewa sun taya Buhari murnar ranar haihuwa. Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Darakta-Janar na Harkokin Watsa Labarai a Gidan Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ne ya wallafa sakon a Facebook.

Kara karanta wannan

'Ka kawo cigaba a Najeriya': Jonathan ya tura sakon yabo da Buhari ya cika 82

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin Arewa sun taya Buhari murna

Shugaban gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya ya bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin abin koyi ga miliyoyin 'yan Najeriya saboda rikon amanarsa da kishinsa.

Inuwa Yahaya ya ce rayuwar Buhari ta kasance cike da sadaukarwa domin ganin Najeriya ta samu nasarori a fannoni daban-daban.

"A lokacin da ka cika wannan shekaru (82), a madadin gwamnatin jihar Gombe da gwamnonin Arewa, mun shiga cikin sahun 'yan Najeriya wajen taya ka murna."

- Shugaban gwamnonin Arewa

Gwamnoni sun yi addua'a ga Buhari

Gwamnonin Arewa sun roki Allah ya kara wa Buhari lafiya da tsawon rai domin ci gaba da taimakawa Najeriya wajen tabbatar da zaman lafiya.

"Muna addu’a Allah ya albarkace ka da hikima da ƙarfin zuciya domin ka ci gaba da bayar da gudunmawa wajen cigaban kasa."

- Shugaban gwamnonin Arewa

Tun a safiyar yau Talata da shugaba Buhari ya cika shekaru 82 ya fara samun sakon taya murna daga ciki da wajen Najeriya.

Kara karanta wannan

Abba ya nada kwamishioni 6, hadimin da aka tsige zai dawo gwamnatin Kano

Shekaru 82: Jonathan ya taya Buhari murna

A wani rahoton, Legit ta wallafa cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya taya Muhammadu Buhari murnar cika shekaru 82.

Rahotanni sun nuna cewa shugaba Goodluck Jonathan ya yi addu'ar Allah ya cigaba da ba Muhammadu Buhari lafiya da nisan kwana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng