Manyan Malaman Izala da Shugaba Tinubu Ya Ba Mukamai a Gwamnatinsa

Manyan Malaman Izala da Shugaba Tinubu Ya Ba Mukamai a Gwamnatinsa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada wasu malamai a cikin gwamnatinsa ciki har da masu alaka da kungiyar Izala.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nada wasu fitattun malaman Izala a gwamnatinsa, wadanda ke da tasiri a bangarorin ilimi da addini a Najeriya.

Farfesa Abdullahi Sale Usman 'Pakistan', fitaccen malami kuma shugaban JIBWIS na Kano, ya zama sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON).

Malamai
Malaman da suka samu mukami a gwamnatin Tinubu. Hoto: Professor Salisu Shehu|NAHCON
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit Hausa ta kawo muku bayanai game da malaman Izala da mukaman da suka samu a sabuwar gwamnati ta Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Farfesa Abdullahi Sale Usman

A watan Agustan 2024 mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa an nada Farfesa Abdullahi Sale Usman a matsayin shugaban NAHCON.

Kara karanta wannan

Shugaban kasar Jamus ya sauka a Najeriya, zai gana da Tinubu

Farfesa Abdullahi Sale Usman (Pakistan), wanda aka fi sani da ƙwarewarsa a harkokin aikin Hajji, ya fara aiki a NAHCON ne bayan majalisar kasa ta tabbatar da nadin sa.

Wannan ya zo ne bayan shugaban kasa ya kori tsohon shugaban hukumar, Jalal Ahmed Arabi, wanda ke fuskantar bincike daga hukumar EFCC kan almundahana da kudin aikin Hajji.

Tarihi da kwarewar Farfesa Pakistan

Farfesa Usman ya kammala karatunsa a Jami’ar Madinah da Jami’ar Peshawar a Pakistan, ya samu digiri a fannonin addini da harkokin zamantakewa.

A baya, ya shugabanci hukumar alhazai ta jihar Kano, ya samu nasarorin shirya aikin Hajji ga mafi yawan alhazai a Najeriya kamar yadda Bayo Onanuga ya sanar.

Addu’ar Izala ga shugaban NAHCON

Kungiyar Izala ta JIBWIS, karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta taya Farfesa Abdullahi Sale Usman samun shugabancin NAHCON

Kungiyar Izala ta yi kira da a taya sabon shugaba da addu'a a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Za a zamanantar da hudubar Juma'a a masallacin Abuja, an kara limamai 5

"A madadin Ƙungiyar JIBWIS muna taya shi Murna tare addu’an Allah ya masa jagora, ya bashi ikon yin adalci, ya bashi nasara akan dukkan lamuran sa, yasa a gama lafiya.
Muna kira ga jama’a da ku sanya shi a cikin addu’oin ku, Allah ya masa jagora."

- Kungiyar Izala

Kalubalen da ke gaban shugaban NAHCON

Sabon shugaban hukumar NAHCON zai iya fuskantar kalubale da dama, musamman wajen bunkasa aikin Hajji da tabbatar da adalci a tsakanin alhazai daga jihohi daban-daban na Najeriya.

Haka zalika ana ganin malamin zai iya fuskantar kalubale ta inda za a saka masa ido wajen gudanar da ayyuka kasancewar an kori wanda ya gaba ce shi saboda almundahana.

Wasu kuma za su so ganin an samu saukin kujerar hajji ganin tsadar da ta yi a yanzu.

2. Farfesa Salisu Shehu

Wani babban nadin da ya jawo hankali shi ne na Farfesa Salisu Shehu, wanda aka nada a matsayin shugaban hukumar NERDC.

Kara karanta wannan

Daga dawowa Najeriya, Tinubu ya shiga yin nade naden mukami a hukumar raya Arewa

Farfesa Salisu Shehu, wanda ke da tarihi mai kyau a fannin ilimi, ya kasance jagora wajen samar da cigaba a bangaren ilimi da zamantakewa.

Tarihi da gudunmawar Farfesa Salisu Shehu

Farfesa Shehu ya taba rike mukamai daban-daban a jami'o'i wanda a yanzu yake rike da shugabancin jami'ar Al-Istiqamah a Kano.

Malamin ya shahara wajen koyarwa da gudanar da bincike a fannin ilimin zamantakewar dan’adam.

Alakar Farfesa Salisu Shehu da Izala

Duk da cewa Farfesa Salisu Shehu ba ya kungiyar Izala dumu-dumu kamar Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya kasance wanda ake yi wa kallo a matsayin dan kungiyar.

Hakan kuma na zuwa ne kasancewar ya hada akida iri daya da ta 'yan Izala kuma yana mu'amala ta addini tare da su tun Sheikh Ja'afar Adam yana raye.

Muhawarar Abduljabbar Kabara a shekarar 2021

Farfesa Shehu ya yi fice a 2021 lokacin da ya zama alkalin muhawarar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu malaman Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi rabon mukamai, ya ba malamin musulunci matsayi a gwamnatin tarayya

Daily Trust ta wallafa cewa Farfesa Salisu Shehu ya yi hukunci da cewa Malam Abduljabbar bai amsa tambayoyin da aka yi masa yadda ya kamata bayan mukabalar.

3. Sheikh Mohammed Bn Othman

Kwanakin baya Bola Tinubu ya nada Sheikh Mohammed Bn Othman a matsayin daya daga cikin kwamishinoin hukumar NAHCON na kasa.

Malamin musuluncin da yake zaune a Kano ya na cikin wadanda ake dangantawa da kungiyar Izala kuma ya yi fice sosai har a wajen Najeriya.

Fatan da ake yi wa malaman a gwamnatin Tinubu

Nadin malaman Izala a manyan mukamai ya tabbatar da tasirin kungiyar a fadin Najeriya da harkar gwamnati.

Duk da kalubalen da za su fuskanta, akwai fatan cewa za su yi amfani da damar wajen kawo cigaba ga Najeriya.

Wani dan agajin Izala a jihar Gombe, Ibrahim Abdullahi ya ce yana fatan ganin canji a harkokin aikin Hajji da Sheikh Pakistan zai jagoranta a bana.

Kara karanta wannan

Za a yi aikin sama da Naira Tiriliyan 4 a masarautar Arewa da ta nada Tinubu Jagaba

An nada limamai 5 a masallacin Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta sanar da karin limamai biyar a Masallacin Abuja.

An ruwaito cewa limaman da aka kara sun hada da mazauna garin Abuja da kuma masu ziyara daga jihohi daban-daban lokaci bayan lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng