'Dan Shekara 100 Ya Auri Mai Shekaru 102, Sun Kafa Tarihi a Duniya

'Dan Shekara 100 Ya Auri Mai Shekaru 102, Sun Kafa Tarihi a Duniya

  • Bernie Littman, mai shekaru 100 da Marjorie Fiterman, mai shekaru 102 sun kafa tarihi a matsayin ma’aurata mafi tsufa a duniya
  • Ma'auratan sun hadu a wurin zama na tsofaffi inda soyayyarsu ta fara bayan sun rasa abokan aurensu na farko
  • Taron aurensu ya samu halartar iyalansu da dama a wani dakin taro na wurin da suke zama kuma a nan soyayyarsu ta fara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Labarin auren Bernie Littman da Marjorie Fiterman ya tabbatar da cewa shekaru ba su hana soyayya.

Mata da mijin da suka haura shekaru 100 sun kafa tarihi a duniya a matsayin ma’aurata mafi tsufa

Ma'aurata
Ma'aurata mafi tsufa a duniya. Hoto: Guinness World Records
Asali: Facebook

'Yan shekara 100 sun yi aure

Guinness World Records ta bayyanawa duniya daurin aurensu a ranar Talata bayan sun shafe shekaru kusan 10 suna soyayya da juna.

Kara karanta wannan

An kashe 'yan bindigar da suka daure babban ma'aikaci a cikin rami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bernie Littman, mai shekaru 100, da Marjorie Fiterman, mai shekaru 102 sun shafe fiye da shekaru 60 tare da abokan rayuwarsu na farko kafin su rasu

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa masoyan sun daura aure tun ranar 19 ga Mayu bayan soyayya mai shekara tara.

Yadda ma'aurata mafi tsufa suka fara soyayya

Littman da Fiterman sun bayyana cewa soyayyar su ta samo asali daga wata liyafa ta musamman da aka shirya a gidan tsofaffin da suke zama.

Marjorie ta ce buttermilk ne sirrin tsawon rayuwarta, yayin da Littman ya bayyana cewa karatu da kasancewa cikin nishaɗi su ne sirrinsa.

Duk da cewa sun kasance a Jami’ar Pennsylvania a lokaci guda shekaru da suka gabata, ba su taɓa haɗuwa ba sai bayan rayuwar su ta yi tsawon shekaru.

'Yan uwa da abokai sun shaida aure

Bikin aurensu ya samu halartar 'yan uwa da abokai ciki har da dangin Littman da dama inda aka gudanar da abubuwan al'ada.

Kara karanta wannan

Bayan fafutukar shekaru 22: Kotu ta ba malamin da aka kora a aiki nasara

Bernie ya ce haɗuwarsa da Marjorie wani alheri ne daga Allah, kuma ba zai manta ranar da soyayyar su ta fara ba.

A daya bangaren, Marjorie ta ce ranar farko da suka hadu ita ce ranar da soyayyarsu ta fara kulluwa.

'Yar fim za ta fara hada aure a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa yawan ƴan mata a gari babu mijin aure ya jawo hankalin jarumar Nollywood, Chinonso Ukah.

'Yar wasan kwaikwayon ta shirya kaddamar da sabuwar manhajar haɗa ƴan mata da samari soyayyar gaskiya da za ta kai ga aure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng