Babban Malami na 3 Ya Rasu a Arewa Cikin Kasa da Mako 1
- Gwamnatin jihar Neja ta yi ta'aziyyar rasuwar babban limamin Minna, Sheikh Ibrahim Isa Fari a yau Lahadi, 17 ga watan Nuwamba
- Gwamna Muhammad Umaru Bago ya bayyana cewa rasuwar Sheikh Ibrahim Isa Fari rashi ne ga dukkan al'ummar Musulmi a Najeriya
- Bincike ya nuna cewa rasuwar malamin ita ce ta uku cikin mutuwar manyan malamai da aka samu a Arewacin Najeriya a mako daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Al'ummar jihar Neja sun tafka babban rashi yayin da limamin Minna, Sheikh Ibrahim Isa Fari ya kwanta dama.
Gwamnatin Neja ta yi ta'aziyyar rasuwar limamin a safiyar yau Lahadi inda ta ce rashin ya shafi dukkan al'ummar Musulmi.
Legit ta tatttaro bayanai kan rasuwar malamin ne a cikin wani sako da gwamna Umaru Muhammad Bago ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban limamin Minna ya rasu
Gwamna Umaru Muhammad Bago na jihar Neja ya nuna damuwa kan rasuwar limamin Minna, Sheikh Ibrahim Isa Fari.
Gwamnan ya ce Sheikh Ibrahim Isa Fari ya kasance wanda ya karantar da soyayya da hadin kai tsakanin al'umma.
A karkashin haka, Umaru Bago ya ce rasuwar malamin babban rashi ne ga mutanen Neja da al'ummar Musulmi.
"Marigayin ya karar da rayuwarsa wajen yin hidima ga addinin Musulunci.
Tabbas za a yi kewar shawara mai kyau da hikimomi da malamin ke bayarwa ga al'umma yayin rayuwarsa."
Gwamna Bago yana fatan Allah ya gafartawa Sheikh Ibrahim Isa Fari, ya sanya shi a Aljannar Firdausi."
- Gwamnatin Neja
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Sheikh Ibrahim Fari ya shafe sama da shekaru 20 yana limanci a Minna kuma ya rasu yana da shekaru 93.
Kafin rasuwar Sheikh Ibrahim Fari, an rasa babban limamin Izala a Bauchi da fitaccen malamin Kur'ani a Gombe.
Shugaban Izala a Kebbi ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Izala da Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ke jagoranta ta sanar da rasuwar shugaban gudanarwanta.
Rahotanni da suka fito sun nuna cewa Sheikh Shua'ibu Muhammad Sarkin Fawa ya rasu ne bayan jinya a gadon asibiti a Sokoto.
Asali: Legit.ng