Kano: Jiga Jigan Najeriya Sun Hallara domin Auren Ƴar Kwankwaso da Ɗan Mangal

Kano: Jiga Jigan Najeriya Sun Hallara domin Auren Ƴar Kwankwaso da Ɗan Mangal

  • Manyan baki sun fara isa Kano domin shaida auren yar Sanata Rabi'u Kwankwaso da za a daura a gobe Asabar, 16 ga watan Nuwamba
  • Tsofaffin gwamnoni daga jihohi daban daban sun isa Kano yayin da jagoran NNPP ya karɓe su a gidansa bayan kammala sallar Juma'a
  • Za a daura auren Dr Aisha Rabi'u Musa Kwankwaso ne da Fahad Dahiru Mangal a fadar mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Manyan baki sun dura Kano domin shaida daurin auren Dr Aisha Rabi'u Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal.

Tsofaffin gwamnoni daga jihohi da dama da sauran manyan yan siyasa a Najeriya sun isa jihar Kano a yau Jumu'a.

Kwankwaso
Baki sun isa Kano auren yar Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Hadimin Sanata Rabi'u Kwankwaso, Saifullahi Hassan ne ya wallafa yadda aka karbi bakin a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Manyan Najeriya da suka hallara auren yar Kwankwaso da dan Mangal a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Auren yar Kwankwaso: Baki sun isa Kano

Tsofaffin gwamnoni da suka hada da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmud Shinkafi sun isa Kano domin auren Aisha Rabi'u Kwankwaso.

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Victor Attah tsohon gwamnan jihar Kebbi, Adamu Aliero sun hallara.

Haka zalika tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Igbinedion, tsohon gwamnan jihar Imo, Achika Udenwa duk sun samu isa Kano.

Karin baki da suka isa Kano

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, Sanata Abdul Ningi na cikin waɗanda suka isa jihar Kano.

Shugaban Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sheikh Muhammadu Kabir Haruna Gombe sun isa Kano domin daurin auren.

Kwankwaso ya karbi baki a gidansa

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf da sauran jiga jigan NNPP ke karɓar baki a Kano.

Bikin Dr Aisha Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal ya zamo matattara da tsofaffin yan siyasa da dama za su hadu da juna.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya zama waliyyin ango, an bayyana sadakin diyar Kwankwaso

Budurwa ta ce tana son auren Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wata budurwa ta bayyana irin tsananin so da take yi wa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Matashiyar mai suna Balkisu ta ce tana son sakon ya isa wurin shugaban kasa Bola Tinubu saboda tana son shi da aure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng