Babban Malami Na 2 Ya Cika a Yau, Jagora a Kungiyar Izala Ya Rasu a Kasar Waje

Babban Malami Na 2 Ya Cika a Yau, Jagora a Kungiyar Izala Ya Rasu a Kasar Waje

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Bauchi na nuni da cewa kungiyar Izala ta rasa babban limamin masallacin Gwallaga
  • Shugaban Izala na Bauchi, Dr Zubairu Abubakar Madaki ne ya fitar da sanarwar rasuwar Imam Ibrahim Idris a yammacin yau
  • Bincike ya tabbatar da cewa Imam Ibrahim Idris ya yi fama da rashin lafiya sosai wanda har ta kai ga kwantar da shi a kasar waje
  • Awanni kafin nan kuma an rasa Gwani Muhammad Sani wanda ya yi fice wajen koyar da karatun Kur'ani a yankin jihar Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Shugaban Izala na jihar Bauchi, Dr Zubairu Abubakar Madaki ya sanar da rasuwar babban limamin masallacin Gwallaga.

Marigayi Imam Ibrahim Idris ne limamin babban masallacin Izala da ke unguwar Gwallaga a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Gogaggen malamin Musulunci a Arewa ya rasu, shugaban gwamnoni ya yi jimami

Imam Idris
Limamin Izala a Bauchi ya rasu. Hoto: Jibwis Bauchi
Asali: Facebook

Dr Zubairu Abubakar Madaki ya fitar da sanarwar ne a cikin wani sako da shafin JIBWIS Bauchi ya wallafa a kafar Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban malamin Izala ya rasu

Kungiyar Izala ta sanar da rasuwar babba limamin masallacin Gwallaga bayan fama da jinya da ya yi.

Rahotanni sun nuna cewa Imam Ibrahim Idris na cikin wadanda suka yi gwagwarmayar kafa kungiyar Izala a tarihi.

"Muna sanar da rasuwar babban limamin masallacin Gwallaga, Imam Ibrahim Idris bayan jinya da ya yi a kasar Egypt.
Muna rokon Allah ya gafarta masa, yasa aljanna ta zamo mokoma a gare shi."

- JIBWIS Bauchi

Sheikh Pantami ya yi jajen rasuwar Imam Idris

Sheikh Isa Ali Pantami ya shiga jerin yan uwa Musulmi wajen yin ta'aziyyar rasuwar Imam Ibrahim Idris.

Pantami ya wallafa a Facebook cewa Imam Idris ya kasance dattijo mai hakuri, sanyin hali, nagarta da son jama'a a duk inda yake.

Kara karanta wannan

Wata 1 da birne matarsa, wani fitaccen dan wasan kwallon kafar Najeriya ya rasu

Malamai a ciki da wajen kungiyar Izala a Najeriya na cigaba da tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin.

Malamin addini ya rasu a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa safiyar ranar Laraba aka sanar da rasuwar shahararren malamin addinin Musulunci, Gwani Muhammad Sani a jihar Gombe.

An ruwaito cewa Sheikh Gwani Muhammad Sani ya shafe shekaru yana karantar da ɗalibai Alkur'ani daga dukkan sassan Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng