Gogaggen Malamin Musulunci a Arewa Ya Rasu, Shugaban Gwamnoni Ya yi Jimami

Gogaggen Malamin Musulunci a Arewa Ya Rasu, Shugaban Gwamnoni Ya yi Jimami

  • A safiyar ranar Laraba aka sanar da rasuwar shahararren malamin addinin Musulunci, Gwani Muhammad Sani a jihar Gombe
  • An ruwaito cewa Sheikh Gwani Muhammad Sani ya shafe shekaru yana karantar da ɗalibai Alkur'ani daga dukkan sassan Arewacin Najeriya
  • Wani daga cikin dalibansa ya tabbatar da cewa an yi masa salla a safiyar yau da misalin karfe 11:00 a kofar gidansa da ke garin Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - A yau aka wayi gari da rasuwar malamin addinin Musulunci, Gwani Muhammad Sani a jihar Gombe.

Shugaban gwamnonin Arewa, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya shiga cikin dimbin al'ummar Musulmi da suka nuna alhini kan rasuwar malamin.

Gwani Sani
Malamin Musulunci ya rasu a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya wallafa a Facebook cewa mutuwar malamin ta bar gibi babba.

Kara karanta wannan

Babban malami na 2 ya cika a yau, jagora a kungiyar Izala ya rasu a kasar waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin addini ya rasu a Gombe

Marigayi Sheikh Gwani Muhammad Sani da ya shahara da karantar da Alkur'ani ya rasu a jihar Gombe.

An yi sallar gawar marigayin a kofar gidansa da ke Kwanar Alheri a jihar Gombe kamar yadda addini ya tanadar.

Gwamna ya yi jimanin rasuwar Gwani Sani

Gwamnan jihar Gombe ya bayyana cewa rasuwar gwani Muhammad Sani ta bar gibi babba a karatun tsangaya a Arewa.

Inuwa Yahaya ya ce Gwani Sani malamin malamai ne kuma ya karantar da dimbin mutane Alkur'ani.

Gwamnan ya isar da sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, ɗalibansa a cikin sakon da Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a Facebook.

Dankwambo ya yi jimamin gwani Sani

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya ce Gwani Muhammad Sani ya kasance fitila ga al'umma.

Ibrahim Dankwambo ya ce yana fatan Allah SWT ya sa halayensa na alheri su bi shi kuma Alkur'ani ya haskaka kabarinsa.

Kara karanta wannan

EFCC: 'Yadda wani gwamna a Najeriya ya tura miliyoyin Naira zuwa asusun ɗan canji'

Legit ta zanta da Iliyasu Ali

Wani mai karatun allo, Iliyasu Ali da ya shafe sama da shekaru 18 tare da Gwani Sani ya ce malamin ya yaye mahaddata masu tarin yawa.

Iliyasu Ali ya ce shi ma ya tura mutane sama da hudu da suka yi haddar Kur'ani a tsangayar Gwani Sani.

An damfari malamin addini a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci a Legas, Sheikh Abdulrasheed Alaseye, ya fada hannun 'yan damfara, ya rasa N351,169.

Rahotanni na nuni da cewa Sheikh Alaseye ya biya kudin rajista da sauran kudi domin zama dillalin kamfanin, amma sai suka ci gaba da neman kari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng