Shugaban Izala Ya Rasu, Al’ummar Musulmi Sun Shiga Jimami

Shugaban Izala Ya Rasu, Al’ummar Musulmi Sun Shiga Jimami

  • Kungiyar Izala da Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ke jagoranta ta sanar da rasuwar shugaban gudanarwanta
  • Rahotanni da suka fito sun nuna cewa Sheikh Shua'ibu Muhammad Sarkin Fawa ya rasu ne bayan jinya a gadon asibiti
  • Tuni al'ummar Musulmi suka shiga jimami da tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da kungiyar Izalar Jos

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Kungiyar Izala karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ta yi babban rashi.

Izala mai hedikwata a birnin Jos ta rasa shugaban gudanarwa a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya.

Shugaban Izala
Shugaban Izala ya rasu. Hoto: Jibiws Gombe State
Asali: Facebook

Shafin JIBWIS Gombe na kungiyar Izalar Jos ne ya sanar da rasuwar Sheikh Shuaibu Muhammad Sarkin Fawa a kafar Facebook.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi ta'aziyyar yan maulidi 150 da ake fargabar sun mutu a hadarin jirgi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Izala a Kebbi ya rasu

Rahotanni na tabbatar da cewa Allah ya yi wa shugaban gudanarwar Izala mai hedikwata a Jos na jihar Kebbi.

Sheikh Shua'ibu Muhammad ya rasu ne a wani asibiti a jihar Sokoto sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Malamin ya kasance na gaba gaba a harkokin addini a jihar Kebbi kuma yana cikin wadanda suka jagoranci alhazai aikin Hajjin bana.

Mutane na jimamin rashin shugaban Izala

Al'umma da dama sun nuna damuwa kan rashin babban malamin musamman lura da gudunmawar da yake bayarwa ga addini.

Zaidu Bala ya wallafa bidiyon marigayin a shafin Facebook yayin aikin Hajji inda ya masa fatan Allah ya gafarta masa zunubansa.

Haka zalika Huzaifa Kasimu Kamba ya wallafa sakon ta'aziyyar rasuwar malamin a shafin Facebook inda ya roki Allah ya gafarta masa.

Kara karanta wannan

Kungiya ta fadawa Tinubu ribar da zai samu idan ya sasanta rikicin masarautar Kano

Malamin addini ya rasu a Jos

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Zakariyya Adam Alhassan Jos ya rigamu gidan gaskiya.

Malam Zakariyya Adam Alhassan ya kasance daya daga cikin malamai da suke da ƙoƙari wajen shiga ƙauyuka domin isar da sakon Musulunci.

Malaman addini daga jihohi da dama sun isar da sakon ta'aziyyar rasuwar Sheikh Zakariyya Adam ga iyalansa da al'ummar Musulmi baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng