‘Zai Kara Aure?’: Al’umma Sun Bayyana Ra’ayoyi kan Sakin Seaman Abbas

‘Zai Kara Aure?’: Al’umma Sun Bayyana Ra’ayoyi kan Sakin Seaman Abbas

  • A yau ne wani karamin sojan ruwan Najeriya da ke zargi an tsare tsawon shekaru shida ya samu yancin fitowa
  • Sai dai a bayan fitowa da shi da aka yi, matar sojan ta yi ikirarin cewa rundunar sojin Najeriya ta kore shi daga aiki
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu daga cikin abubuwan da yan Najeriya suka fada bayan sakin Abbas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Matar sojan saman Najeriya, Seaman Abbas da ta ce an daure shi shekaru shida ta bayyana cewa ya samu yanci.

Fitowar Seaman Abbas ta ja hankulan al'umma musamman zargin cewa rundunar soja ta kore shi daga aiki.

Kara karanta wannan

Seaman Abbas: Rundunar soji ta sallami sojan ruwa da aka 'tsare' har shekaru 6

Seamna Abbas
Yan Najeriya sun yi magana kan Seaman Abbas. Hoto: Brekete Family
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu daga cikin abubuwan da yan Najeriya suka mayar da hankali a kai bayan sakin sojan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai sauran aiki inji Yazeed

Wani mai amfani da kafar Facebook, Yazeed Salisu ya ce ya kamata a cigaba da addu'a domin har yanzu akwai sojan da yake kulle ba a ji labarinsa ba.

Yazeed Salisu ya wallafa a Facebook cewa akwai wata mata, Ramlat Ridwan da ta kai kukan cewa mijinta sojan ruwa ya shiga garari ranar da aka shigar da kukan kama Seaman Abbas.

Karofi ya ce Seamnan Abbas ya kara aure

Wani mai amfani da kafar Facebook mai suna Elder Karofi ya wallafa cewa ya kamata Seaman Abbas ya kara mata domin ta rika taya Hussaina aiki.

Elder Karofi mai yaki da bautar da maza da mata su kan yi, ya yi alkawarin cewa idan Seaman Abbas ya amince da haka to zai biya masa kudin sadaki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami’an gidan yari 4, ta fadi dalili

Yamai ya ce a tausayawa Seaman Abbas

Yamai Muhammad ya bayyana cewa akwai rashin tausayi wajen masu yin kira ga Seaman Abbas ya kara aure.

Yamai ya wallafa a Facebook cewa rashin wayewa ne da kauyanci mayar da jarrabawar da Seaman Abbas ya shiga abin wasa da raha.

Yan Najeriya da dama sun taya Seaman Abbas murnar samun 'yanci tare da matarsa mai suna Hussaina.

Shi kuwa wani mai suna Phoenix a shafin X ya ce idan dai tsohon sojan ya nemi kara aure, su da kan su za su hana a yi wa Hussaina kishiya.

"Idan seaman Abbas ya mata kishiya har gida za mu je mu zane mata shi" - @Citizen_IQ

NEF ta yi magana kan Seaman Abbas

A wani rahoton, kun ji cewa Kungiyar Northern Elders Forum ta bayyana takaicin labarin cin zarafin wani jami'in rundunar sojan ruwa, Seaman Abbas.

Jami'in hulda da jama'a a NEF, AbdulAzeez Suleiman ya ce yadda aka samu labarin Husaina Iliyasu kan cin zarafin mijinta ya jawo damuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng