'Ba haka ba ne,' Sarkin Benin Ya Ƙaryata APC kan Zargin Yakar PDP a Zaben Edo

'Ba haka ba ne,' Sarkin Benin Ya Ƙaryata APC kan Zargin Yakar PDP a Zaben Edo

  • Mai martaba Oba na Benin, Oba Ewuare II ya yi raddi ga Adams Oshiomhole a gaban wasu jiga jigan jami'yyar APC a Najeriya
  • Adams Oshiomhole da manyan yan APC sun dura fadar mai martaba Oba na Benin ne domin mika godiya bayan zaben Edo
  • A lokacin taron, Oshiomhole ya yi ikirarin tun a shekarar 2016 Oban ya gargade shi a kan dauko Godwin Obaseki amma ya ki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Oba na Benin ya yi martani ga jigon APC a jihar Edo, Adams Oshiomhole yayin wata ziyara da suka kai masa a ranar Lahadi.

Adams Oshiomhole ya ce Oba Ewuare II ya gargade shi tun a shekarar 2016 a kan kawo Godwin Obaseki.

Kara karanta wannan

“Bai taba cin zabe a Edo ba;” Mataimakin gwamna ya yi shagube ga gwamnansa

Admas
Oba na Benin ya ci gyaran jigon APC. Hoto: Adams Oshimhole
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa nan take Oba Ewuare II ya yi maratani ga Adams Oshiomhole kan maganar da ya fada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar APC ta je fadar Sarkin Benin

APC ta haɗa babbar tawaga zuwa fadar Oba na Benin domin masa godiya a kan zaben gwamna da ya gabata a Edo.

Tawagar ta haɗa da tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da zaɓaɓɓen gwamnan Edo, Monday Okpebholo.

Tsohon shugaban APC ya roki gafarar Sarkin Benin

Jigon APC, Adams Oshiomhole ya sunkuya kasa ya ce ba zai mike ba har sai Oba na Benin ya yafe masa kuskuren da ya yi a 2016.

Adams Oshiomhole ya ce a 2016 ya kawo maganar tsayar da Godwin Obaseki takara amma sarkin ya ki amincewa amma kuma ya ki yarda da shawarar sarkin.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya dura kan gwamna, ya ce ya mutu murus a siyasar Najeriya

Sarkin Benin ya ci gyaran Oshiomhole

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa nan take Oba Ewuare II ya ce sam ba su yi haka da Adams Oshiomhole a shekarar 2016 ba.

Basaraken ya ce shi ba zai so cigaba da yawan surutu a siyasa ba, kuma ya kafa shaida kan cewa bai fadi haka ga Kwamred ba.

PDP ta nuna fargaba kan zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus ya zargi jami'yyar APC da yaki da demokradiyya a zaben Edo na ranar Asabar.

Uche ya ce akwai alamun cewa APC na son lalata dimokuraɗiyyar Najeriya wanda ba lallai a samu karfin gwiwar zaben 2027 ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng