Babban Sarki a Jiha Ya Rasu bayan Shafe Shekaru 42 a kan Karaga
- An wayi gari da rashin mai martaba Owa-Obokun na Ijesaland, Oba Gabriel Adekunle Aromolan a jihar Osun
- Oba Gabriel Adekunle Aromolan yana cikin manyan sarakuna a kasar Yarabawa da ke kudancin tarayyar Najeriya
- Ya fara sarauta ne tun Fabrairun shekarar 1982 wanda hakan ke nuni da cewa ya shafe shekara 42 kan karagar mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - Jihar Osun ta yi babban rashi yayin da mai martaba Oba Gabriel Adekunle Aromolan ya kwanta dama a yau Alhamis.
An ruwaito cewa Oba Gabriel Adekunle Aromolan shi ne shugaban majalisar sarakuna na jihar Osun.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Asiwaju na Ijesaland, Yinka Fasuyi ne ya fitar da sanarwar rasuwar babban basaraken.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban sarki a jihar Osun ya rasu
A yau Alhamis, 12 ga watan Satumba aka shiga jimamin rasuwar Sarkin Osun, Oba Gabriel Adekunle Aromolan.
An tabbatar da rasuwar marigayi Oba Gabriel Adekunle Aromolan bayan an yada jita jitar cewa ya kwanta dama a safiyar yau.
Shekarun da sarkin Osun ya yi a karaga
Jaridar the Nation ta wallafa cewa a ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar 1982 aka naɗa Oba Gabriel sarauta.
Bisa kididdiga, hakan ya nuna cewa Oba Gabriel Adekunle Aromolan ya shafe shekaru 42 a kan karaga kafin rasuwarsa.
Halayen sarki Gabriel Adekunle Aromolan
Yayin da yake sanar da rasuwar Oba Gabriel Adekunle Aromolan, Yinka Fasuyi ya ce mutum ne mai jarumta kuma mai karamci.
A saboda haka ne Yinka Fasuyi ya ce dukkan jama'ar Osun sun shiga jimami bayan rasuwar Oba Gabriel Adekunle Aromolan.
Atiku ya yi jimamin Oba Gabriel
A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubukar ya aika sakon ta'aziyya ga al'ummar kasar Ijesha da ke jihar Osun bisa rasuwar babban sarkinsu, Owa Obokun.
A yau Alhamis, 12 ga watan Satumbar 2024 ne aka sanar da rasuwar Owa Obokun na Ijeshaland, Oba Gabriel Aromolaran.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana marigayi Aromolaran a matsayin jajirtaccen basarake kuma suruki na gari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng