Maganar Sheikh Jingir da Wasu Abubuwa da suka Tayar da Kura kan Gwamnatin Tinubu
- An samu abubuwa da dama da suka faru a kan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka jawo ce-ce-ku-ce a makon da ya wuce
- Daga ciki akwai maganar da shugaban majalisar malaman Izala mai hedikwata a Jos ya yi a kan karin kudin man fetur da aka yi
- A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku abubuwan da suka faru a gwamnatin Bola Tinubu da suka dauki hankalin al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fuskanci abubuwa da dama da suka jawo ce-ce-ku-ce a makon da ya wuce.
Maganar da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi da maganar ajiye aiki da Ajuri Ngelale ya yi sun tayar da kura a kafafen sadarwa.
A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku wasu daga cikin muhimman abubuwa uku da suka faru a makon da ya wuce kan gwamantin.
Maganar Sheikh Jingir kan kudin fetur
A ranar Juma'a da ta wuce ne Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana cewa makiya tikitin Musulmi da Musulmi ne suka kara kudin mai a Najeriya.
Legit ta ruwaito cewa malamin ya ce idan Tinubu ya dawo Najeriya zai iya kawo saukin lamarin sai dai maganar Sheikh Jingir ta jawo ce-ce-ku-ce sosai.
Ajuri ya ajiye aiki a fadar shugaban kasa
Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya sanar da ajiye aiki a ranar Asabar inda ya bayyana cewa zai fuskanci wasu abubuwa na rashin lafiyan makusantansa.
Ajiye aikin Ngalele ya tayar da kura musamman yadda wasu jaridu suka bankado cewa an samu rashin jituwa ne a fadar shugaban kasa.
Tinubu ya ce karin kudin fetur dole ne
Daga cikin abubuwan da suka tayar da kura akwai maganar da Bola Tinubu ya yiwa yan Najeriya mazauna kasar Sin kan karin kudin mai.
A yayin da yan Najeriya ke jiran samun sauki amma sai Bola Tinubu ya ce karin kudin mai ya zama dole idan ana son gina kasa kamar Sin.
Kukah ya bukaci rage kudin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa Rabaran Matthew Hassan Kukah ya yi kira ga gwamnatin tarayya a rage kudin man fetur da aka kara da ya kara tsada.
Faston ya ce a halin yanzu yan Najeriya na fama da yunwa saboda haka ya kamata a tausaya musu a rage kudin man fetur ko za a samu sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng