Obasanjo Ya Fadi Muhimman Halayen Mahaifiyar Yar’adua yayin Ta’aziyya

Obasanjo Ya Fadi Muhimman Halayen Mahaifiyar Yar’adua yayin Ta’aziyya

  • Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya je jihar Katsina domin ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar Umaru Musa Yar'adua
  • Yayin ta'aziyyar, Olusegun Obasanjo ya bayyana wasu halayen kirki na marigayiya Hajiya Dada Musa Yar'adua
  • Cif Olusegun Obasanjo ya samu rakiyar manyan yan siyasa daga ciki da wajen jihar Katsina yayin ziyarar ta'aziyyar da ya kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya je jihar Katsina domin ta'aziyyar rasuwar Hajiya Dada Musa Yar'adua.

Hajiya Dada Musa ta kasance mahaifiya ce ga tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'adua wanda ya yi mulki bayan saukar Obasanjo.

Obasanjo
Obasanjo ya je ta'aziyyar Dada Yar'adua. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Olusegun Obasanjo ya yi ne cikin sakon da jami'in yada labaran jihar Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Tarewar hafsoshin tsaro a Arewa ta zo da alheri, sojoji sun yi rugu rugu da miyagu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halayen mahaifiyar Yar'adua masu kyau

Yayin ta'aziyyar, Cif Olusegun Obasanjo ya ce za a tuna Hajiya Dada da halin kasancewa uwa ce mai ba da kulawar da ta wuce misali.

Obasanjo ya kara da cewa Hajiya Dada tana da halin kyautatawa da karbar baki cikin mutunci da kuma yin kirki ga al'umma.

Gwamna Radda ya yi godiya ga Obasanjo

Gwamna Dikko Umaru Radda ya mika godiya mai dimbin yawa ga Obasanjo bisa ta'aziyyar da yazo musu.

Radda ya ce suna matuƙar godiya bisa tunawa da su da Obasanjo ya yi a lokacin da suka yi babban rashin.

Wadanda suka raka Obasanjo ta'aziyya

Cikin tawagar da suka raka Obasanjo akwai Murtala Shehu Yar'adua da tsohon hadimin Obasanjo, Inuwa Baba.

A ƙarshe, Obasanjo ya yi fatan Allah ya gafarta wa Hajiya Dada Musa Yar'adua da kuma Allah ya ba mutane hakurin rashin.

Kara karanta wannan

"Ya yi ta'aziyya": Bashir Ahmad ya fadi dalilin rashin zuwan Buhari jana'izar Dada

Saraki ya yi ta'aziyyar Hajiya Dada

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya tuno haduwarsa ta karshe da Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi Umaru Musa Yar’adua.

An ruwaito cewa Hajiya Dada ta rasu tana da shekaru 102 a yammacin ranar Litinin a asibitin koyarwa na Katsina bayan ta yi fama da rashin lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng