Bayan Samun Agajin N19m, Iyayen 'Yan 4 Sun Samu N5m daga Gidauniyar Otedola

Bayan Samun Agajin N19m, Iyayen 'Yan 4 Sun Samu N5m daga Gidauniyar Otedola

  • Bayan taya wasu iyayen 'yan hudu neman tallafin jama'a, iyayen jariran na ci gaba da samun taimakon daidaikun jama'a da kamfanoni
  • A wannan karon, gidauniya fitaccen mai kudi, Femi Otedola ce ta mika tallafin Naira Miliyan 5 ga iyayen jariran domin saukaka masu
  • Kyautar ta wannan lokaci ta biyo bayan Naira Miliyan 19 da aka tattarawa iyayen 'yan hudun ganin su na bukatar tallafin kula da jariran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas - 'Yan hudun da aka haifawa Sodiq Olayode na kara samun tallafin jama'a, inda har yanzu ake mikawa iyayensu tallafin kudi.

A ranar Litinin ne gidauniyar Femi Otedola ta tallafawa iyalan da kudi na Naira Miliyan 5 domin ci gaba da lura da yaransu hudu rigis da aka haifa.

Kara karanta wannan

"Ko mutum 1 ba a kashe a lokacin zanga zanga ba," Inji rundunar 'yan sandan Kano

Sodiq
Iyayen yan hudu sun samu tallafin N5m daga gidauniyar Otedola Hoto: @jamysax
Asali: Twitter

Wani mai suna James da ya fara nemawa iyalan 'yan hudun taimako, ya wallafa a shafinsa na X cewa gidauniyar Otedola ta ba wa iyayen tallafin, har da tallafin karatu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidauniyar Otedola ta bada tallafin karatu

Gidauniyar Femi Otedola da ta shahara wajen tallafawa 'yan Najeriya ta fuskoki da dama ta dauki nauyin karatun yara biyu daga cikin yara shida na iyalan Mista Olayode.

The Cable ta wallafa cewa sun samu tallafi ne bayan an nema masu taimako wajen kula da yan hudun da matar gidan, Abiodun ta haifa.

Philip Akinola da ya mika kyautar N5m da tallafin karatu har jami'a ga yara biyu na iyalan, ya ce an yi haka ne bayan karanta labarinsu da yadda su ka nemi daukin a jaridu.

Otedola ya musanta raba tallafi kudi

Kara karanta wannan

"Naira miliyan 8.5 ake biya," tsohon dan majalisa ya fallasa kudin gudanarwarsu duk wata

A baya mun ruwaito cewa hamshakin mai kudi, Femi Otedola ya musanta labarin da aka rika yadawa kan cewa ya na neman bayanan jama'a domin ba su tallafi.

A wani rubutu da aka yi a shafin Facebook mai dauke da sunan Otedola mai mabiya 17,000, an gargadi jama'a da su guji bayar da bayanansu ga wadanda su ka nema.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.