“Na Hakura”: An Fusata Aliko Dangote, Ya Fallasa Wadanda Suka Fi Shi Tsabar Kudi a Najeriya

“Na Hakura”: An Fusata Aliko Dangote, Ya Fallasa Wadanda Suka Fi Shi Tsabar Kudi a Najeriya

  • Attajirin Afrika dan asalin jihar Kano, Alhaji Aliko Dangote, ya ce akwai wasu 'yan Najeriya da suka fi shi madarar kudi
  • Dangote ya ce akwai takaici idan ya ji ana cewa shi kadai yake juya kasuwa a Najeriya alhalin ansan ba gaskiya bane
  • Ya yi kira ga sauran masu kudin kasar da su kwaso kudin da suka boye a kasashen ketare su zo su zuba jari a cikin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Fitaccen attajirin Afrika, Aliko Dangote ya ce akwai wasu 'yan Najeriya da suka fi shi tumbatsar arziki.

A yayin jawabi ga 'yan majalisar wakilan Najeriya da suka zagaya matatarsa a Legas ranar Asabar, attajirin ya ce cike da rashin adalci ake zarginsa da juya kasuwa shi kaɗai.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Yan sanda sun dakume kwararren barawo ya na tsakiyar sata a Kaduna

Aliko Dangote ya yi magana kan masu zarginsa da hadama
Aliko Dangote ya ce akwai wadanda suka fi shi madarar kudi a Najeriya. Hoto: @DangoteGroup
Asali: Facebook

Dangote ya koka kan zargin da ake masa

Daily Trust ta ruwaito cewa Aliko Dangote ya ce laƙabawa kamfanoninsa sunan masu juya kasuwa su kaɗai yana da taɓa zuciya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Dangote ya ƙara da cewa wannan ya sa ya janye shirinsa na saka hannun jari a masana'antar tama da karafar kasar.

A cewar attajirin:

"Juya kasuwa kai ɗaya shi ne idan ka hana jama'a, ka toshesu ta hanyoyin shari'a. Sanin kowa ne duk abin da kamfanin Dangote ke yi yana zuwa kai tsaye ne ga jama'a.

"Akwai wadanda suka fi ni kudi" - Dangote

Jaridar Premium Times ya buƙaci 'yan Najeriya da su saka hannun jari a masana'antar domin taimakawa wurin haɓaka tattalin arzikin ƙasar.

"A bar sauran 'yan Najeriya su je su yi. Ba mu kaɗai bane 'yan Najeriya a nan. Akwai wasu 'yan Najeriya da suka fi mu kudi.

Kara karanta wannan

Dangote ya fara shirin sayar da matatar man fetur dinsa, an samu bayanai

"Ya kamata a barsu su tattaro kudin nan da suka boye a Dubai da sauran sassan duniya tare da saka su a ƙasarsu ta gado."

- Aliko Dangote.

Dangote ya kalubanci NMDPRA kan dizal

A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya ƙalubalanci NMDPRA kan cewa matatarsa na samar da dizal marar kyau.

Wannan martanin ya zo ne bayan da shugaban hukumar NMDPRA ya bayyana cewa dizal ɗin da matatar Dangote ke tacewa bai kai ingancin wanda Najeriya ke shigowa da shi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.