Abubuwa 4 da Ya Kamata Ku Sani Kan Hon. Ekene Abubakar Adams, Dan Majalisa da Ya Rasu

Abubuwa 4 da Ya Kamata Ku Sani Kan Hon. Ekene Abubakar Adams, Dan Majalisa da Ya Rasu

  • A yau Talata, 16 ga watan Yuli 2024 dan majalisar wakilai, Abubakar Adams Ekene ya rigamu gidan gaskiya
  • Fadar shugaban kasa, gwamnan Kaduna da majalisun Najeriya da yan uwa sun nuna alhini bayan rashin dan majalisar
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku muhimman abubuwan da ya kamata ku sani a kan Abubakar Adams

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yau Talata ne majalisar dokokin Najeriya ta yi rashin daya daga cikin mambobinta da ya fito daga jihar Kaduna.

'Dan majalisar tarayya, Hon. Abubakar Adams Ekene ya rasu a yau ne kwanaki kadan bayan majalisar ta rasa Prince Olaide Akinremi.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta karrama ɗan majalisar da Allah ya yiwa rasuwa yau

Adams Ekene
Abubuwa masu muhimmanci kan dan majalisar da ya rasu. Hoto: Adams Ekene
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku abubuwa masu muhimmanci kan Abubakar Adams kamar yadda kakakin majalisar ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwa masu muhimmanci kan Adams Ekene

1. Yaushe aka haifi Adams Ekene?

Rahotanni na nuni da cewa an haifi dan majalisar mai suna Abubakar Adams Ekene ne a shekarar 1985

Haka zalika dan majalisar ya fito ne daga yankin Chikun da Kajuru a jihar Kaduna kuma yankin yake wakilta a majalisar dokoki.

2. Mukamin Adams Ekene a majalisa

Abubakar Adams Ekene ne ke rike da kwamitin majalisa da ke kula da harkokin wasanni a Najeriya.

Kakakin majalisar, Abbas Tajudeen ya bayyana cewa Adams Ekene ya kawo cigaba sosai a kan harkokin wasanni a Najeriya.

3. Adams Ekene na son wasanni

Daga cikin manyan abubuwan da marigayi Abubakar Adams Ekene yake so akwai harkokin kwallon kafa.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Jagaban, wani ɗan majalisar tarayya daga Kaduna ya mutu

Saboda haka ne ma ɗan majalisar yake da kulob din ƙwallon ƙafa a jihar Kaduna mai suna Kada City FC.

4. Adams Ekene ya rasu a bakin aiki

Tajudeen Abbas ya bayyana cewa majalisa na shirin karbar wakilan Najeriya a wasan Olympics da ake shirin yi a Faris ne labarin rasuwarsa ya iso.

Kuma da ma kafin rasuwar Abubakar Adams Ekene yana jagorancin neman tallafi na kudi ga yan Olympics din Najeriya.

Dan majalisar wakilai ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa Allah ya yi wa dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabun Garki da Babura, Isa Dogonyaro daga jihar Jigawa rasuwa.

Marigayin ya rasu ne da safiyar ranar Jumu'ah, 10 ga watan Mayu a birnin tarayya Abuja bayan fama da gajeruwar jinya da ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng