Rashin Abin Yi: Pantami Zai Taimakawa Matashin da Ya Gama NYSC Babu Aiki

Rashin Abin Yi: Pantami Zai Taimakawa Matashin da Ya Gama NYSC Babu Aiki

  • Babban malamin addinin Musulunci Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi alkawari kawo dauki daga wani matashi da yake neman taimako
  • Matashin mai suna Umar Ibrahim Umar yana neman taimako ne domin fara sana'ar POP bayan kammala karatun a jami'ar FUK
  • Umar Ibrahim Umar ya kasance dan asalin jihar Gombe inda a halin yanzu yake neman yadda zai fadada neman kudi domin inganta rayuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi alkawarin tallafawa wani matashi.

Matashin mai suna Umar Ibrahim Umar ya fara naiman taimako domin fara sana'ar POS bayan kammala jami'a.

Kara karanta wannan

Limami ya shiga matsala kan zuwa aikin hajji babu izinin basarake, an yi masa barazana

Sheikh Pantami
Sheikh Pantami zai taimaki matashi domin fara sana'a. Hoto: @UmarIbrahimUm18|@ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Legit ta gano alkawarin da Sheikh Pantami ya yi cikin wani martani da ya rubuta a shafinsa na X a yau Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alƙawarin Pantami ga Umar Ibrahim Umar

Sheikh Isa Ali Pantami ya rubuta a shafinsa cewa zai ba da gudunmawa ga matashin domin inganta rayuwarsa.

Farfesa Pantami ya ce Ibrahim Umar ya tuntube shi domin ganin ta hanyar da zai ba shi gudunmawa.

Yadda lamarin matashin ya fara

Tun a shekarar 2022 aka rika yaɗa hoton matashin a lokacin da ya dage da fareti a sansanin masu yiwa ƙasa hidima.

Ganin dagewa da yayi wasu suka fara nuna cewa ba lallai ya samu aiki ba idan ya gama hidimar kasa sai dai ya fara sana'ar POS.

Amma a lokacin matashin ya yi martani a shafinsa na X cewa ba ya sana'ar POS, kuma zai cigaba da hidima ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Yobe: Wata matar aure ta soka wa mijinta wuƙa har lahira, ta yi bayanin abin da ya faru

Salihu Tanko Yakasai ne ya jawo hankalin al'umma, su taimakawa Umar.

Ibrahim Umar na neman fara POS

Kasancewar yadda rayuwar yau ta zama, matashin ya fara neman taimako a yanar gizo domin fara sana'ar POS.

Duk da cewa jama'a da dama sun yi yunkurin taimaka masa, amma a yau Laraba ya tabbatar da cewa ya samu gudummawar N282,000.

A halin yanzu, hankula sun karkata zuwa ganin irin gudummawar da Sheikh Pantami zai ba matashin domin inganta rayuwarsa.

Kawun Sheikh Pantami ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin addinin musulunci, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi jimamin mutuwar yayan mahaifiyarsa, Malam Abubakar Audu.

Tsohon ministan Najeriyan ya ce kawun nasa wanda aka fi sani da suna Malam Dankule, Allah ya masa rasuwa ne bayan yana da shekaru 110 a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng