An Yi Babban Rashi a Najeriya, Tsohon Gwamna Ya Kwanta Dama

An Yi Babban Rashi a Najeriya, Tsohon Gwamna Ya Kwanta Dama

  • Rahotanni da suke fitowa sun yi nuni da cewa tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Benue, Adebayo Hameed Lawal ya rasu
  • 'Yar cikinsa mai suna, Yinka Ehahoro ce ta sanar da manema labarai rasuwarsa a safiyar yau Litinin, 24 ga watan Yuni
  • Yinka Ehahoro ta kuma bayyana ranar da za a yiwa AVM Hameed Lawal janaza tare da labarta yadda ya kwanta dama

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamna jihar Benue na mulkin soja, AVM Adebayo Hameed Lawal ya rigamu gidan gaskiya.

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa AVM Adebayo Hameed Lawal ya rasu ne bayan ya cika shekaru 83 a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya nuna yatsa kan 'yan majalisar da ke adawa da shi

Jihar Benue
Tsohon gwamnan Benue na soja ya rasu. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa 'yar AVM Adebayo Hameed ce mai suna Yinka Ehahoro ta sanar da rasuwarsa a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukaman da tsohon gwamnan ya rike

Daga cikin manyan mukamai da AVM Adebayo Hameed Lawal (Mai ritaya) ya rike akwai gwamna a jihar Benue daga 1978 zuwa 1979.

Har ila yau marigayi AVM Adebayo Hameed Lawal ya rike ministan wasanni da harkokin matasa a Najeriya.

Marigayi AVM Adebayo a gidan soja

Tun a shekarar 1963 AVM Adebayo ya fara aiki da rundunar sojin saman Najeriya inda ya samu horo a kasar Jamus, rahoton Vanguard.

A cikin shekarun da ya yi yana aiki, ya rike kwamandan rundunar sojin sama a jihohin Kano, Enugu, Benue da Fatakwal.

Rayuwar Adebayo Lawal bayan ritaya

Bayan AVM Adebayo Hameed Lawal ya yi ritaya ya shiga harkokin kasuwanci da taimakon al'umma.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

AVM Adebayo ya rasu ne a jiya Lahadi yana bacci kuma za a masa jazana ne a yau Litinin kamar yadda iyalansa suka sanar.

An kashe mutane a Benue

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mahara a kan babura sun farmaki kauyen Gugur a karamar hukumar Katsina Ala da ke jihar Binuwai inda su ka kashe mutane shida.

Wakilin yankin a majalisar jiha, Jonathan Agbidye ya tabbatar da harin sai dai ya ce harin na ramuwar gayya ne, kuma yanzu kura ta lafa kowa ya ci gaba da ayyukansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng