Ghali Na’Abba: Tsohon Shugaban Majalisa Ya Bar Duniya Babu Gida Sai N250,000 a Banki

Ghali Na’Abba: Tsohon Shugaban Majalisa Ya Bar Duniya Babu Gida Sai N250,000 a Banki

  • Ghali Umar Na’Abba bai bar duniya a matsayin hamshakin attajiri ba duk da matsayin da ya rike a siyasa
  • Tsohon ‘dan majalisar ya zama na hudu a duk Najeriya da ya rike shugaban majalisar wakilai a 1999
  • Wani wanda ya san marigayin, ya ce a lokacin da Na’Abba ya rasu, N250, 000 kacal aka samu a asusunsa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ghali Umar Na’Abba ya yi shekaru kusan hudu a matsayin shugaban majalisar wakilai, amma ya mutu bai da tarin dukiya.

Bayanai sun fito game da dukiyar da Hon. Ghali Umar Na’Abba ya bari a duniya bayan ya rasu a karshen Disamban shekarar 2023 da ta wuce.

Ghali Na’Abba
Ghali Umar Na’Abba ya rasu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Da aka yi magana da wani na kusa da Ghali Na’Abba a shirin “Rigar Kaya”, ya ce marigayin bai biyewa tara abin duniya a rayuwa ba.

Kara karanta wannan

Duk da adawarsa, mataki 1 da Shugaba Tinubu ya dauka ya jawo Atiku ya yaba masa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da babban mukamin da ya rike, Hussain Na’Abba ya ce Hon. Ghali Umar Na’Abba da kyar ya rika kokarin biyawa kan shi kudin asibiti.

Daily Nigerian ta rahoto Hussain Na’abba ya na mai ikirarin a lokacin da ‘dan siyasar ya cika, N250, 000 kadai aka samu a asusun bankinsa.

"Ghali Na'Abba bai tara dukiya ba" - Hussain Na’Abba

“Ya mutu bai da gida a Kano, Abuja, ko Kaduna.
Asusun bankinsa kuma ya nuna N250, 000 kacal yake da shi kafin ya rasu.
Bayan ‘ya iskan gari sun kona gidansa a Kano, sai ya rika rabewa a gidan mahaifiyarsa a duk lokacin da ya ziyarci garin Kano."

- Hussain Na’Abba

Ghali Na'Abba ya rasa gidansa

Ghali Na’Abba ya samu kyakkyawar shaida kamar yadda wannan mutum wanda ya san shi ya tabbatar da aka zanta da shi a yanar gizon.

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Minista ya magantu bayan Tinubu ya kira shi zuwa Villa, bayanai sun fito

Marigayin yana da akidar taimakon talakawa, Hussain Na’abba ya ce wannan ya sa Rt. Hon. Na’Abba bai yi kokarin tara kayan kele-kele ba.

Ganin yadda aka kona gidan shi, tsohon ‘dan majalisar bai ji dadin yadda talakawa su ka juya masa baya ba, bai kuma nemi sake gina gida ba.

Za a iya ba Godwin Emefiele N100m

A wani labarin na dabam, sai aka ji tsohon gwamnan CBN ya yi galaba a kan hukumar EFCC da ya shigar da kara a wata kotun tarayya.

Alkali ya ce a biya Godwin Emefiele diyyar N100m saboda zaluntarsa, amma EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta ce babu inda ta saba doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng