Dan Najeriya Ya Caccaki Bankinsa Bayan Sun Ba Shi Jabun Kudi Na Yuro 5000

Dan Najeriya Ya Caccaki Bankinsa Bayan Sun Ba Shi Jabun Kudi Na Yuro 5000

  • Wani dan Najeriya ya koka bayan wani bankin kasuwanci ya ba shi kuɗin jabu na Yuro 5,000 wanda sun kai kimanin N4.2m
  • Mutumin ya ce ya ciro kuɗin ne daga reshen bankin domin ya ba wani abokinsa da zai yi tafiya zuwa Birtaniya
  • Fusataccen mutumin ya ce an gano Yuro 5000 da bankin ya bayar na jabu ne bayan abokinsa ya kai wajen canjin kuɗi na Euro Change FX.

Wani ɗan Najeriya ya fusata inda ya caccaki wani bankin kasuwanci bayan sun ba shi kuɗaɗen jabu.

A jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na twitter, ya bayyana cewa an ba shi tsabar kuɗi Yuro 5,000 na jabu, kuma ya gano ne kawai lokacin da abokinsa ya je canja kuɗin zuwa fam.

Dan Najeriya ya koka bayan banki ya ba shi kudin jabu
Dan Najeriya ya zargi bankinsa da ba shi kudin jabu Hoto: Twitter/@Dblinkz and Getty Images/Bloomberg
Asali: Twitter

Mutumin wanda ya fusata ya ce ya ajiye kuɗin Yuro 5000 ne a reshen bankin da ke kan titin Ali Akilu, a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Kwastoma Ya Yi Yunkurin Kona Banki Bayan Ya Nemi Kudadensa Ya Rasa

Sai dai, an gaya masa cewa ya je babban reshen bankin lokacin da ya buƙaci cire kuɗin domin amfani da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Banki ya ba wani mutumi jabun kuɗi

Lokacin da ya je babban reshen bankin ne aka ba shi jabun kuɗin.

Mutumin da ke amfani da sunan Legendary Papi a Twitter, ya ce kuɗaɗen ya same su ne ta hanyar halal.

A kalamansa:

"Daga nan na je babban reshen bankin domin ciro Yuro 5000 waɗanda aka bani su cikin takardun Yuro 500. Dalilin ciro kuɗin shi ne ina son na ba abokina da zai koma Ingila ya taimaka min ya canja su zuwa Fam domin na biya kuɗin makaranta, kawai yana zuwa @eurochangeFX sai aka ƙwace kuɗin saboda an gano cewa na jabu ne."

Wane martani ƴan Najeriya suka yi?

@Credo_promotion ya rubuta:

"Kamata ya yi manajan bankin nan da ya baka jabun kuɗin yana gidan gyaran hali a yanzu."

Kara karanta wannan

Wani Jirgi Ya Yi Hatsari Bayan Mai Ya Kare, Ana Fargabar Mutane da Yawa Sun Mutu a Jihar PDP

@ChuksEricE ya rubuta:

"Dubi wai bankin Najeriya yana ba kwastomansu kuɗin jabu. Lallai akwai ƙasa."

@Obilala_2000 ya rubuta:

"Babu wani sabon abu ba ne. Na taɓa cire kudin jabu daga ATM na Banki, da na shiga na yi korafi sai suka ce babu wani abu da za su iya yi a kai, domin watakila na canza kudin ne tsakanin ATM da harabar bankin. Abubuwa da yawa na hauka suna faruwa a Najeriya."

Matashi Ya Bude Asusun Banki Na Yayan da Zai Haifa

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya shiri domin ganin ƴaƴan da za a haifa masa sun yi rayuwa cikin wadata.

Matashin dai ya ajiye kuɗade har Naira biliyan 2 inda ya ke son adana musu Naira biliyan 122 zuwa girmansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng