Matashiyar Uwa Da Katoton Danta Sun Girgiza Intanet Da Tikar Rawa Kamar Abokai, Bidiyon Ya Yadu

Matashiyar Uwa Da Katoton Danta Sun Girgiza Intanet Da Tikar Rawa Kamar Abokai, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata matashiyar mahaifiya da danta sun girgiza intanet bayan sake wani faifan bidiyo a TikTok
  • @ivo_official ya wallafa faifan bidiyon inda aka gano kyakkyawar mahaifiya da danta suna tikar rawa
  • Mutane da dama sun yi martani inda suke fatan samun irin wannan mu'amala tsakaninsu da iyayensu

Wani kayataccen faifan bidiyo ya burge mutane bayan ganin matashiyar uwa da katoton danta na tikar rawa.

Faifan bidiyon da aka gano mahaifiya 'yar Najeriya da danta wanda @ivo_official ya wallafa a Tiktok ya girgiza kafofin sada zumunta.

Matashiyar uwa na tikar rawa da danta kamar abokai, bidiyon ya yadu
Faifan Bidiyon Da Wata Matashiyar Uwa Da Katoton Danta Ke Tikar Rawa. Hoto: @ivo_official1/TikTok.
Asali: TikTok

A faifan bidiyon, mahaifiyar da danta na tikar rawa tare da bin wani sautin kida a Tiktok.

Hakan ya nuna irin kusanci da dan ke da shi da mahaifiyarsa yayin da suke rawa a lokaci guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Assha: Kaka ya siyar da jikarsa N700k a wata, shi da dillaliya sun shiga hannu

Yadda suke yin ko wani motsi a lokaci guda shi ya burge mutane inda suka yi ta sa musu san barka, Legit.ng ta tattaro.

Jama'a da dama sun yabi uwar da danta ganin yadda suke mu'amala kamar abokai ba tare da tsangwama daga uwar ba.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Faifan bidiyon ya jawo martanin jama'a inda mutane da dama suka yi martani tare da yadawa a kafafen sada zumunta.

Meye jama'a ke cewa kan faifan bidiyon?

@Jarvis:

"Kun yi kyau."

@Rita:

"Ya yi kyau mama."

@user3021501676160:

"Ta hadu sosai."

@kelvinamihere456:

"Ina son ku gaba dayanku, ya yi kyau mama."

@user9851143703403chika:

"Wannan abu ya kashe ni da dadi, uwa da danta."

@user1910035637857:

"Ina son wannar matan, ta na inganta abubuwa."

@anappa21:

"Ina jin farin cikin kallo, mama kin ba da mamaki a wannan rawar."

Matashi Na Mamakin Yadda Matashiyar Uwa Ta Haife Shi

Kara karanta wannan

“Ina Biyan Miliyan 1.8 Duk Wata: Matashi Ya Nuna Dan Karamin Gidan Da Yake Haya a Landan, Ciki Ya Hadu

A wani labarin, wani matashi ya girgiza kafar sadarwa ta intanet bayan wallafa bidiyonsa da mahaifiyarsa a TikTok su na kallon-kallo da ita tare da mamakin ita ce mahaifiyarsa.

A cikin faifan bidiyon an gano matashin na mamakin yadda aka yi 'yar karamar mahaifiyarsa ta haife shi katoto da shi wanda har ya shiga kwaleji don kara karatu.

Faifan bidiyon ya jawo cece-kuce inda mutane da dama ke mamakin yadda matashiyar matar ta haifi yaro kato kamar wannan inda da yawa suka yi tsammanin budurwarsa ce ba mahaifiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel