'Ƴar Najeriya Ta Koma Tallar Ruwa Bayan Ta Koma Nahiyar Turai, Bidiyonta Ya Yadu
- Wata mata ƴar Najeriya wacce ta koma ƙasar waje da zama ta zama abin cece-kuce bayan ta sanya wani sabon bidiyo a soshiyal midiya
- A cikin ɗan ƙaramin bidiyon da yaɗu a yanar gizo, an nuna matar tana tallar ruwan roba a wani titi a nahiyar Turai
- Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani sosai akan bidiyon inda da dama daga cikinsu suka ƙarfafa mata gwiwa cewa kada ta sare
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata mata ƴar Najeriya da ta koma nahiyar Turai ta burge masu amfani da yanar gizo sosai bayan bidiyonta ya bayyana a manhajar TikTok.
A cikin bidiyon wanda ya yaɗu, an nuna matar tana tallar ruwan roba a wani titi a nahiyar Turai domin neman na kanta.
Ta sanya robobin ruwan a cikin wani kwano wanda ta ɗauka a kanta tana siyarwa da mutane masu wucewa.
Martanin ƴan soshiyal midiya yayin da ƴar Najeriya ta koma tallar ruwa a Turai
A yayin da mutane da dama suka caccaketa kan tallar ruwan da take yi, wasu kuwa yaba mata suka yi saboda jajircewar da ta yi wajen neman na kanta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga kaɗan daga ciki waɗanda Legit.ng ta tattaro nan ƙasa:
conafzgqk8y ya rubuta:
"Mun cika zaƙewa wajen yin abubuwa, menene kuma wannan."
@ezekieleffiok ya rubuta:
"Kin san yadda ake neman kuɗi. Nagode."
@ras_b.k ya rubuta:
"Ruwa rayuwa ne a wannan lokacin da rana ta gama soya kowa."
@omoscothegreat ya rubuta:
"Hakan na nufin dai ƴan Afirika ko ina suka je tare da talaucinsu su ke tafiya."
@seyifunmi75 ta rubuta:
"Ku rabu da ita kasuwancinta take yi kuma hakan yafi ace bara take yi."
@sugargirl244 ta rubuta:
Dalilin Da Ya Sanya 'Yan Bindiga Suka Kwamushe Ni, Babban Boka Ya Yi Bayani Bayan Ya Shaki Iskar 'Yanci
"Yanzu sai wani daga ƙauyensu ya kirata ya ce ta turo masa kuɗi."
An Kwace Kilishin 'Yar Najeriya a Filin Jirgi
A wani labarin kuma wata budurwa ƴar Najeriya wacce tafiya ta kama zuwa ƙasar Amurka ta koka kan yadda jami'an tsaro suka ƙwace mata kilishi a filin jirgi.
Budurwar dai ta yi guzurin kilishin ne domin ta riƙa kashe kwaɗai a ƙasar Amurka amma sai jami'an tsaron suka ba ta cikas a filin jirgi.
Asali: Legit.ng