Ma'aikaciyar Otal Ta Dawo Da $70,000 Da Ta Tsinta, Mutane Da Dama Sun Yaba Mata
- Wata budurwa ƴar Najeriya mai halin kirki, Kekwaaru Ngozi Mary, ta dawo da kuɗin da ta tsinta har $70,000 (N54,355,000)
- Budurwar wacce ma'aikaciya ce a otal ɗin 'Eko Hotel and Suites' ta yi hakan ne bayan wani mutum ya yarda su a otal ɗin
- Daga cikin ƴan Najeriyan da suka yi martani akan labarin, akwai masu cewa ba za su taɓa yin hakan ba idan da su ne
An yaba wa wata budurwa ƴar Najeriya mai suna, Kekwaaru Ngozi Mary, bisa dawo da tsabar kuɗi har $70,000 (N54,355,000) na wani mutum da ya yarda su.
A cewar rahoton Vanguard, lamarin ya auku ne a otal ɗin 'Eko Hotel and Suites' inda take yin aiki.
Ngozi ta dawo da $70,000 s otal
Budurwar ba ta taɓa ko sisi ba na kuɗin kafin ta dawo da su. Mutane da dama sun bayyana cewa ita ɗin abin misali ce da halin gaskiya a lokacin da ake ciki wanda mutane da dama ba za su iya dawo da kuɗin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da dama sun yi martani kan bidiyonta da aka sanya a TikTok a shafin @voiceofourancestorch. Wasu daga cikin sun yi tir da halin da ta nuna.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin da mutane suka bayyana:
KB D GENTLE ya rubuta:
"Kuɗin sun faɗi a hannun da bai dace ba. da ni ne da tuni ina Dubai yanzu."
Sylvester said:
"Kuna ba ta shawarar ta gudu da kuɗin. Ta ina za ta bi ta wuce da kuɗin, kuna tunanin cewa irin waɗannan ƴan ƙananan otal ɗin ne. Tabbas sai an cafko ta."
Daddy whizzy ya rubuta:
"Kun yi hannun riga da arziƙi."
Blaze said:
"Cikin talauci za ta zauna daga nan har ƙarshen rayuwarta."
salambabalola ya rubuta:
"Ku ɓarayi ne, kuna tunanin cewa idan ta gudu da kuɗin ba za ta kamu ba ne."
Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana
De Kelly said:
"A talauce za ki mutu, nawa ya baki, ya wuce N2m? kolo, Allah ka taimake ni na samu irin wannan damar."
@esosaleonard said:
"Akwai mutanen da a duniyar nan da ba ruwansu da kayan wani. Su haka rayuwarsu take."
Mahajjaciya Ta Tsinci N56m a Saudiyya
A wani laɓarin kuma, wata mahajjaciya a ƙasa mai tsarki ta yi tsintuwar N56m a yayin gudanar da aikin Hajji a ƙasar Saudiyya.
Mahajjaciyar wacce ta fito daga ƙaramar hukumar Bungudu ta miƙa kuɗin hannun hukuma ba tare da taɓa ko sisi ba.
Asali: Legit.ng