"Kada Ki Bari A Kama Ki": Dalibar Jami'a Ta Nuna Salon Satar Jarabawa a Soshiyal Midiya, Bidiyon Ya Yadu
- Wata ɗalibar jami'ar jihar Ebonyi ta nuna kayan satar jarabawarta cikin izza a soshiyal midiya ba tare da tsoro ba
- Kayan satar jarabawar na ta sun ƙunshi amshoshi da aka rubuta cikin ƙananan rubutu waɗanda ta shirya yin amfani da su
- Wasu masu amfani da soshiyal midiya sun gargaɗe ta da kada ta jefa kanta cikin matsala a dalilin wallafar da ta yi, yayin da wasu suka ɗauki wallafar a matsayin barkwanci
Ezinne, wata ɗalibar jami'ar jihar Ebonyi (EBSU), cikin izza ta nuna kayan da za ta yi satar jarabawa da su a soshiyal midiya.
A cikin bidiyon, Ezinne ta nuna kayayyakin satar jarabawar da ta tanada, waɗanda aka rubuta su da ƙananan rubutu yayin ta ke shirin yin amfani da su a ɗakin jarabawa.
"Ta Sauya Lambobinta": Bayan Gama Lashe Kudin Saurayin Da Ya Dauki Nauyin Karatunta, Budurwa Ta Auri Wani Daban
Ta yi dariyar cewa jami'a waje na wanda ya iya allonsa ya wanke sannan ta yi nuni da cewa wallafar da ta yi na zuwa ne ana saura minti 10 a fara jarabawar.
'Yan Soshiyal midiya sun yi martani
Mutane da dama sun jiye mata tsoron kada bidiyonta ya sanya ta a cikin matsala.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Callyglitz||Jewelry ta rubuta: "
Ahhhh... rubutun ki yana da girma. Da ace ƙawata ce ta rubuta maki, zai ɗauke a cikin faifofi uku."
Oyinkansola ya rubuta:
"Kina kiran matsala ga kanki, ina addu'ar kada ace su ce sai kin dawo kin sake rubuta dukkanin jarabawoyin da kika yi, saboda baki san iya inda bidiyon nan zai je ba @Zinny."
Hookby_ceec ta rubuta:
"Ba zan iya yin haka ba ooooo, tare na ke karatu da ƙawaye na, sannan mu taru mu tattauna wata ƙila wani ya manta da wani abun saboda a makarantar mu kora ce kai tsaye idan aka kama mutum."
Estarr ta rubuta:
"Na taɓa yi sau ɗaya inda da kyar na tsallake darasin saboda ban iya amfani da ita ba, sannan na ɓata lokaci mai yawa wajen rubuta shirme."
Sai dai, bayan an sake bibiyar shafin ɗalibar na @ezinne_6 a manhajar TikTok, ta goge bidiyon na ta wanda ta ɗora.
Matashi Ya Rikice Wajen Duba Sakamakon JAMB
A wani labarin kuma, wani matashi ya shiga halin ɗimuwa lokacin da yake ƙoƙarin duba sakamakon jarabawar JAMB.
Matashin dai hannuwansa sun kiɗime da kakkarwa cikin tsoron rashin sanin abinda idanuwansa za su gane masa idan ya duba jarabawar.
Asali: Legit.ng