Matar Aure Ta Samu Matsala Da Mijinta Bayan Ta Bari Garjejen Kato Ya Yi Mata Tausa

Matar Aure Ta Samu Matsala Da Mijinta Bayan Ta Bari Garjejen Kato Ya Yi Mata Tausa

  • Wani magidanci ya daina cin abincin matarsa saboda ta bari wani ƙato ya yi mata tausa lokacin da suka je wajen ɗimama jiki
  • Magaidancin ya kuma daina yi wa matarsa magana wanda hakan ya sanya matar shiga damuwa ta garzaya soshiyal midiya ta bayyana abinda ke faruwa
  • Amma matar ta bayyana cewa mijin nata wata budurwa ce ta yi masa tausa a wajen kuma ba ta ji haushin hakan ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matar aure ta samu matsala da mijinta bayan ta bari wani ƙato ya yi mata tausa lokacin da suka je wajen ɗimama jiki.

A cikin saƙon ɓoye kai wanda aka sanya a shafin @XBrianDennis a manhajar Twitter, matar ta bayyana cewa sun je wajen ne tare da mijinta.

A taƙaice, matar ta bayyana cewa mijinta shi ma wata budurwa ce ta yi masa tausa a wajen kuma ba ta ji haushi ba dangane da hakan.

Kara karanta wannan

“Kaina Ya Kulle”: Budurwa Ta Shiga Rudani Yayin da Saurayinta Ya Tura Mata N500k Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amanarta

Magidanci ya fusata bayan matarsa ta bari namiji ya yi mata tausa
Magidancin ya fusata inda ya daina cin abincinta Hoto: Getty Images/Cavan Images/Elena Gonzale Hontoria and Izusek.
Asali: Getty Images

Lokacin da suka kammala ɗimama jikin suna kan hanyarsu ta komawa gida, matar ta gayawa mijinta cewa ƙato ne ya yi mata tausa a wajen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamanta:

"Wata budurwa ce ta yi masa tausa sannan wani namiji ya yi min tausa. Na gaya masa cewa namiji ne ya yi min tausa lokacin da mu ke kan hanyar dawowa gida, kawai sai ya kama fushi da ni."

Ta bayyana cewa ya fusata tun daga lokacin ya inda ya daina yi mata magana da cin abincinta saboda tausar da ta bari aka yi mata.

Labarin ya yaɗu sosai inda mutane suka yi ta bayyana mabanbantan ra'ayoyi a Twitter.

Martanin masu amfani da Twitter

@XBrianDennis ya rubuta:

"Idan ni da matata mu ka je wajen ɗimama jiki, mace za ta yi mana tausa mu duka. Eh na yarda ni munafuki ne sai me to?"

Kara karanta wannan

"Kana Bin Sa’ar Uwarka”: Uba Ya Kama Dansa Mai Shekaru 21 a Gidan Hajiyar Birni, Bidiyon Ya Yadu

@DC___100x commented:

"Gaskiya ba zan iya bari wani garjejen namijo ya yi wa matata tausa ba."

@dollarpapii ya rubuta:

"Dama can yana ta neman hanyar da za su yi faɗa ne."

@Emperor35322512 ya rubuta:

"Ke ma in banda abinki ai namiji bai kamata ya yi miki tausa ba."

Magidanci Ya Yi Barazanar Sakin Matarsa

A wani labarin kuma, wani magidanci ya fusata matuƙa bayan matarsa ta ƙi yrda ta ƙara haihuwa da shi.

Magidancin wanda suka haihu sau biyar tare da matarsa ya yi barazanar ɗatse igiyar auren da ke tsakaninsu idan bata bari sun ƙara samun iri ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng