Budurwa Ta Fasa Auren Attajirin Saurayinta Ana Dab Da Biki, Ta Bayyana Dalilanta

Budurwa Ta Fasa Auren Attajirin Saurayinta Ana Dab Da Biki, Ta Bayyana Dalilanta

  • Wata matashiyar budurwa ƴar Najeriya ta bayyana halin da ta tsinci kanta bayan ta rabu da attajirin wanda za ta aura
  • A cewarta sai da ta rufe ido daga ganin cewa yana da dukiya domin tsira daga halin ƙuncin da yake sanyata a ciki
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani akan bidiyon, inda da yawansu suka tausasa mata zuciya saboda halin da ta shiga

Wata budurwa mai amfani da sunan @thatmelaninbaby a TikTok, ta bayyana dalilanta na cewa ta fasa auren saurayinta ana sauran wata uku a ɗaura musu aure.

A cikin wani bidiyo da ta sanya a TikTok, budurwar ta bayyana cewa bata taɓa tunanin za su rabu da wanda za ta aura ɗin ba ana saura ƴan watanni bikinsu.

Budurwa ta rabu da saurayinta ana dab da biki
Budurwa tace farin cikinta ya fi abun duniya muhimmanci Hoto: @thatmelaninbaby
Asali: TikTok

Ta tuna yadda ƙawayenta suka riƙa ganin laifinta saboda ta rabu da attajiri a maimakon ta tsaya ta jure wuyar da ta ke sha a tarayyarsu.

Kara karanta wannan

Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo

Sai dai, budurwar ta yi bayanin cewa ba za ta iya ci gaba da jure wahalar da ta ke sha ba, wacce ta sanya ta kasa mayar da hankali kan kasuwancinta wanda har ya kai ga ya kusa durkushe wa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da ƙalubalen da ta ke fuskanta ta bayyana cewa komai na tafiya mata akan daidai sannan ta nuna muhimmancin fifita yi wa zuciya abinda ta ke so fiye da ƙwadayin abun duniya.

Mutane sun yi sharhi bayan budurwa ta fasa auren attajiri

Bidiyon ya ɗauki hankula sosai a TikTok, inda mutane da dama suka bayyana yadda suka rabu da masoyansu ana dab da bikinsu.

@Juneau65 ta rubuta:

"Ƴan'uwan saurayin da ƴar'uwata za ta aura sun sanya an fasa biki ana saura sati ɗaya. Yanzu haka ta auri likita suna zaune cikin farin ciki da ƴaƴansu tagwaye maza guda biyu."

Kara karanta wannan

Mmesoma Ejikeme Ta Sharbi Kuka a Yayin Wayar Tarho, Ta Dauki Alkawarin Bayar Da Hakuri, Sabon Bidiyo Ya Bayyana

@jerrybryan ya rubuta:

"Ai ba auren mai kuɗin ba ne matsala. Abinda zai biyo baya shi ne damuwar."

@CJ ta rubuta:

"Yanzu haka abinda na ke fuskanta kenan. Na mayar da sadaki na kafin a ɗaura aure. Da muguwar rawa gwara ƙin tashi. Na san yadda kike ji ƴa'uwa."

Magidanci Ya Yi Wuff Da Mata Uku a Tare

A wani labarin kuma, wani magidanci ya yi wuff da mata uku a lokaci ɗaya domin huce takaici.

Magidancin dai ya auri mata ukun ne a tare bayan matarsa ta farko ta guje shi wanda hakan ya tunzura shi ɗaukar wannan matakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng