"Zai Biya N10m Shigar Ciniki": Attajiri Dan Najeriya Na Neman Wacce Za Ta Haifar Masa Yaro, Zai Biya N20m
- Wani matashi ɗan Najeriya mai hannu da shuni wanda bai kai shekara 30 a duniya ba, yana neman matar da za ta haifar masa ɗa akan tukwicin N20m
- A cewarsa baya son yin aure saboda soyayyar da ya taɓa yi sau ɗaya a rayuwarsa a baya wacce bai ji daɗin rabuwar da suka yi ba
- Bayan N20m da zai bayar a matsayin ladan aikin, wacce ta amince ɗin a ƙasar waje zai kai ta domin haifo jaririn
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani matashi ɗan Najeriya mai shekara 26 wanda ya cire rai da samun soyayya da yin aure, ya bayyana cewa yana neman budurwar da za ta ɗauki ciki ta haifo masa ɗa.
Wani mai amfani da sunan @Wizarab10 a shafin Twitter, wanda ya yi wannan roƙon a maimakon matashin ya yi bayanin cewa duk wacce ta amince za a bata N10m kafin a fara sannan bayan ta haihu a cika mata ragowar N10m ɗin.
Da yake sanya hotunan rubutun da matashin ya yo masa kan wannan buƙatar tasa, @Wizarab10 ya ƙara da cewa a ƙasar waje za a haifi yaron kuma matashin ne zai ɗauki nauyin komai.
Daga cikin hotunan da @Wizarab10 ya sanya, matashin ya bayyana kansa a matsayin mai hannu da shuni wanda yake samun maƙudan kuɗaɗe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar matashin sau ɗaya kawai ya taɓa yin soyayya da gaske a rayuwarsa amma bata haifar da ɗa mai ido ba wanda hakan ya sanya ya ji baya son yin aure.
Sharuɗɗan da ake buƙatar wacce ta amince za ta cika
Ya bayyana cewa dole ne budurwar kada ta wuce shekara 35 sannan ta san da sanin cewa babu wani abu da ya haɗa ta da jaririn sannan ko da nan gaba bata isa ta nemi yaron ba bayan an kammala aikin.
"Duk Da Mahaifiyarsa Ta Ba Shi Baki Ya Dau Dangana": Sabon Ango Ya Nemi Saki a Kotu Kwana 2 Bayan Daurin Aure
Ya ƙara da cewa ita ce zata kula da yaron a watannin farko masu muhimmanci bayan ta haihu sannan bayan ta kammala za a cika mata ragowar N10m.
Matashi Ya Ciyo Bashi Domin Faranta Ran Masoyiyarsa
A wani labarin kuma, wani matashi mai siyar da rai domin nemo suna ya harzaya banki ya ciyo bashi domin ya farantawa rabin ransa rai.
Matashin dai ya ciyo bashin zunzurutun kuɗi har N500k sannan ya ɗamka su a hannun budurwar tasa ta sha shagalinta.
Asali: Legit.ng