“Kamata Ya Yi Namiji Ya Auri Mata Sama Da 2”, In Ji Wani Mutum, Ya Ba Da Dalilansa

“Kamata Ya Yi Namiji Ya Auri Mata Sama Da 2”, In Ji Wani Mutum, Ya Ba Da Dalilansa

  • A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da ya yaɗu a intanet, an ga wani mutum yana bayyana ra'ayinsa da ya janyo cece-kuce game da auren mata sama da ɗaya
  • Mutumin ya ƙalubalanci mazan da ke auren mace ɗaya ko biyu, inda ya yi kira garesu da su yi ƙoƙarin auren uku ko fiye da haka
  • A cewar mutumin, auren mace ɗaya imani ne da wasu suka yi a hakan, kuma yin biyu ma na iya zama da haɗari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da ya yaɗu cikin 'yan kwanakin nan, an ga wani mutum da ya yi maganganu game da aure da suka janyo cece-kuce a yayin da ake tafiya a cikin wata motar haya.

Mutumin, wanda yake magana cikin izza, ya ce a ganinsa kamata ya yi a ce maza su riƙa auren mata uku ko fiye da haka maimakon ɗaya ko biyu kawai.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Maimaita Darasin Yau Ba": Bidiyo Ya Nuna Lakcara Shi Kadai a Aji Dalibai Sun Ki Zuwa

Wani mutum ya bayyana adadin matan da ya kamata a aura
Wani mutum ya ce mata sama da 3 ya kamata mutum ya aura. Hoto: @itisbobby
Asali: TikTok

Dalilin da ya sanya mutumin cewa a auri mata sama da 2

Ya bayyana cewa auren mace ɗaya kacal, wani imani ne na addini da wasu suka yi. Auren biyu kuma akwai haɗari, domin za su iya haɗa kai su cutar da mijin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce amma auren mata uku na da amfani, saboda ɗaya daga cikinsu za ta tona duk irin tuggun da biyun suke shiryawa mijin.

Bugu da ƙari, mutumin ya shawarci maza da su kula da kansu kuma su adana isassun kuɗaɗe. Ya yi iƙirarin cewa yara a yanzu sun fi mayar da hankali ga uwayensu mata.

An tafka Muhawara a kafafen sada zumunta yayin da mutumin ya ba maza shawarar su auri mata fiye da 2

Bidiyon ya janyo cece-kuce a tsakanin masu kallo da ke kafar TikTok, inda wasu suka goyi bayan ra'ayin mutumin, a yayin da wasu kuma ke ganin ko hakan zai iya yiwuwa a zamanin da ake ciki. Ga ra'ayoyin kamar haka:

Kara karanta wannan

Dan Majalisar Jam'iyyar Labour Ya Ba Wa Peter Obi Shawarar Abin Da Ya Dace Ya Yi Wa Tinubu

@kizzystanle ya ce:

"Mace ɗaya ta fi, da farko kuyi tarayya da ita kafin ka aureta domin nazarin halayenta, idan kuka yi aure, dukanku za ku ji daɗin rayuwarku tare."

@tianabella33 ta ce:

"Mutumin ka iya yin rayuwa mai tsawo, sai dai 'ya'yansa ka iya fuskantar matsala, sa'ad da 'yan daki ɗaya daga cikin 'ya'yan matan suka samu ci gaba, sai kaga ana ta jifan juna da sihiri.”

@michaelrich 1 ya ce:

"Ina goyon bayan wannan hakan ."

@charlesquartey2 ya ce:

"Mahaifin mahaifiyata ya auri mata huɗu, kuma ya rayu shekara 103. Mahaifina da ya auri ɗaya, ya rasu tun ina ɗan shekara 13."

Magidanci ya nunawa duniya kyawawan 'ya'yansa mata su 10

Legit.ng a baya ta kawo muku labarin wani magidanci da ya wallafa wani bidiyo na 'ya'yansa mata su 10 da ya ɗau hankula a kafafen sada zumunta.

A cikin bidiyon da magidancin ya ɗora a shafinsa na TikTok, an ga yadda kyawawan 'yan matan ke fitowa ɗaya bayan ɗaya a yayin da ake ci gaba da haskasu a bidiyon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng