"Duk Da Mahaifiyarsa Ta Ba Shi Baki Ya Dau Dangana": Sabon Ango Ya Nemi Saki a Kotu Kwana 2 Bayan Daurin Aure

"Duk Da Mahaifiyarsa Ta Ba Shi Baki Ya Dau Dangana": Sabon Ango Ya Nemi Saki a Kotu Kwana 2 Bayan Daurin Aure

  • Kwana biyu bayan ɗaurin aure, wani ango ya nemi saki saboda rashin ɗa'ar da amaryarsa ta yi wa mahaifiyarsa
  • Matarsa da mahaifiyarsa sun yi rikici a wajen liyafar aurensu wanda ya sanya har suka shararawa juna mari
  • Ya tubure ya ƙi ɗaukar shawarar mahaifiyarsa ta ya ɗauki dangana, angon ya nace cewa sai ya datse igiyar auren da ke tsakaninsa da amaryar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Auren kwana biyu kacal ya tunkuyi dutse bayan da sabon angon ya shigar da ƙara neman saki bisa rashin daraja mahaifiyarsa da matarsa ta yi.

Wani ɗan Najeriya wanda ya karanci ilmin dabbobi, Abdullah A Abdullah, wanda ya wallafa labarin ya bayyana cewa da gaske ya faru sannan ya nemi shawara daga wajen masu amfani da yanar gizo.

Ango ya nemi saki kwana 2 bayan aure
Amaryar dai ta rama marin da surikarta ta yi mata Hoto: Torinews.com
Asali: UGC

Abdullah ya bayyana cewa fushin da angon ya yi ya samo asali ne biyo bayan wani abu da ya faru a wajen liyafar auren shi, wanda ya sanya matarsa da mahaifiyarsa suka mari juna.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba a Sakatariyar PDP

Lamarin ya faru ne bayan wasu baƙi daga ɓangaren mahaifiyar angon sun iso wajen basu samu abinci ba ya ƙare. Ragowar abincin da amaryar ta ajiye domin iyayenta ne kawai ya yi saura.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk haƙurin da mahaiyarsa ta ba shi bai ɗauka ba

Mahaifiyar ta sa sai ta tunkari amaryar inda ta raɗa mata cewa ta taimaka ta ɗan ɗebo mata daga cikin abincin ta ba baƙinta saboda bai dace ba idan aka bari suka koma ba tare da sun sanya wani abu a cikinsu ba duba da sun zo daga nesa ne.

Nan fa amaryar ta shafawa idon ta toka ta ƙi yarda inda tace abincin iyayenta za ta ba. Bayan ta bata baki ta ƙi yarda, sai mahaifiyar tasa ta sanya kwano ta ɗebo abincin da kanta amma sai amaryar ta ƙwace ta mayar da shi cikin kula.

Kara karanta wannan

"Duk Su Na Masifar Ƙaunata": Matashi Mai 'Yan Mata Biyu Ya Rasa Ta Zaba, Ya Koma Neman Taimako

Uwar miji ta shararawa matar ɗan ta mari

Cikin fushi sai uwar mijin ta shararawa matar ɗanta mari, wacce ita kuma ta sanya hannu ta rama. Abdullah ya ce mijin ya samu labarin abinda ya faru inda ya ƙi ɗaukar mataki a wajen sai bayan kwana biyu ya nemi saki a kotu.

Abdullah ya ce ana ta shari'ar sakin sannan angon ya ƙi sauraron haƙurin da mahaifiyarsa ta ba shi na ya manta da komai kawai ya yafe matar tasa.

Matashi Mai Ƴan Mata Biyu Na Neman Shawara

A wani labarin na dabn kuma, wani matashi ya garzaya yanar gizo neman shawara kan budurwar da yakamata ya zaɓa a cikin ƴan matansa biyu da suke soyayya.

Matashin duk suna masifar ƙaunarsa amma guda ɗaya kawao zai iya zaɓa a matsayin abokoyar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng