"Na Koyi Darasi": Matashi Ya Ajiye Aikinsa Mai Gwabi Domin Ya Kasance Da Budurwarsa, Sun Rabu Bayan Sati 2

"Na Koyi Darasi": Matashi Ya Ajiye Aikinsa Mai Gwabi Domin Ya Kasance Da Budurwarsa, Sun Rabu Bayan Sati 2

  • Wani matashi ya ajiye aikinsa a kamfanin man fetur domin ya kasance tare da budurwarsa wacce ke zaune a wani birnin daban, basu daɗe ba suka rabu
  • Ya sanya labarinsa ne a Twitter inda ya yi amfani da #LoveMadeMeDolt, wanda ya yaɗu sosai a manhajar Twitter
  • Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu akan labarin nasa, inda wasu suka tausaya masa yayin da wasu suka caccake shi

So makaho ne wanda baya ji baya gani kuma ya kan sanya mutum ya yi wani abu wanda hankali ba zai ɗauka ba.

Hakan shi ne abinda ya faru da wani matashi wanda ya ajiye aikinsa a wani kamfanin man fetur mai girma a Port Harcourt, domin ya kasance da budurwarsa wacce take a birnin Ibadan.

Matashi ya ajiye aiki saboda budurwarsa
Matashin ya koma cizon yatsa daga baya Hoto: @Phoenix23
Asali: Twitter

Bawani aikin ya samu ba a ƙasa, sannan bai san cewa soyayyar ta su ta kusa zuwa ƙarshe ba.

Kara karanta wannan

"Sai Da Ya Yi Hawaye": Matashiya Ta Ba Direba Mai Kirki N10,000 Bayan Ya Caje Ta N2,500 Duk Da Tsadar Mai

Makahon so ya kai shi ya baro

Matashin wanda yake amfani da sunan @Phoenix23 a Twitter, ya sanya labarinsa ne a kafar ta sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ya yi murabus daga aikin da yake yi mai gwaɓi a kamfanin man fetur ɗin, saboda yana son ya kasance kusa da budurwarsa wacce ke zaune a wani garin daban.

Ya yi fatan cewa idan ya koma Ibadan, za su samu isashshen lokacin da za su raini soyayyarsu ta yi ƙwari sosai.

Sun rabu sati biyu bayan ya bar aikin

Sai dai, abubuwa ba su tafi masa yadda ya tsara su ba. Ya bayyana cewa sun rabu bayan sati biyu kacal da komawarsa Ibadan.

Bai bayyana dalilin da ya sanya suka rabu ba, amma ya yi dana sanin wautar da ya yi ta barin aikinsa.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Da Ke Gab Da Yin Aure Ya Rasa Ransa Sakamakon Nutsewa A Ruwa A Enugu

Matashin ya bayyana cewa ya san ya yi sakarci wajen barin aikinsa saboda soyayya sannan ya buƙaci mutane da kada su yi masa hukunci kan kuskuren da ya aikata.

Za ku iya karanta abinda ya rubuta a nan

Kyakkyawar Budurwa Ta Bar Matashi Da Cizon Yatsa

A wani labarin, wani matashi ya koka bayan wata kyakkyawar budurwa ta tatse masa ƴan kuɗaɗen aljihunsa ta gudu.

Matashin ya tura mata kuɗi ne domin ta kawo masa ziyara, inda kuɗin na zuwa gareta ta watsa shi a kwandon shara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng